Jaridun Jamus sun sake duba rikice-rikice a Afirka
December 30, 2022Za mu fara ne da sharhin da jaridar die tageszeitung ta yi a kan rikicin Habasha mai taken "Karin zaman Lafiya da tsoro tsakanin al'umma, inda ta ce gwamnatin Habasha da 'yan gwagwarmaya na Tigray na hanzarta aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da suka rattaba wa hannu a kai a farkon watan Nuwamba. Amma fargabar sabon yaki na karuwa yayin da kuma kuncin rayuwa ke ta'azzara tsakanin al'umma.
Jaridar ta ci gaba da cewa babbar alama ta zaman lafiya ta wakana a lokacin da a karon farko cikin kusan shekaru biyu jirgin saman Habasha na Ethiopian Airlines ya sauka a Mekelle a ranar Laraba. Gidan talabijin na yankin ya nuna gamuwar 'yan uwa da suka dade a rabe a filin jiragen sama da ke babban birnin yankin da ke neman ballewa na Tigray. An kwan biyu rabon da a jefa bama-bamai a garuruwan da ke karkashin ikon kungiyar TPLF ciki har da Mekelle babban birnin yankin Tigray ba.
Ita kuwa Frankfurter Allgemeine Zeitung, ta duba halin da ake ciki ne a Somaliland bayan tashin hankali da aka fuskanta, inda ta ce a daidai lokacin da Somaliland ke tunawa da wani mummunan yakin basasa, al'ummarta na samun kwanciyar hankali a yanayi na raya fasahar wake-wake da rubuce-rubuce.
Jaridar ta ce bayan yakin basasa a Somaliya da kuma faduwar mulkin kama-karya na Siad Barre, Somaliland ta ayyana 'yancin kai a shekarar 1991, wadda Taiwan ce kadai ta amince da ita a duniya. Tana da takardar kudi na kanta, tana da sojoji da gidajen talabijin da kuma dumbin 'yan kasar da ke da zama a Turai da Amirka da Kanada. Sai dai ga sauran kasashen duniya, ba kasa ce mai cin gashin kanta ba.
Jaridar ta kara da cewa Somaliland kasa ce ta makiyaya. Wannan yana fitowa fili a zanen da ake yi a gidaje da ofisoshi da kantuna. Sannan kuma al'ummarta na ci gaba da raya al'adar wakar baka, saboda har yanzu akasarin jama'a ba su iya karatu ko rubutu ba. Hasali ma suna kyautata al'adar da suka gada daga kakanninsu ta haddace tatsuniyoyi da waka.
Idan muka zo ga jaridar Neue Zürcher Zeitung kuwa, ta yi sharhinta ne kan Sudan mai taken: " Wadanda suka bace a juyin juya hali", inda ta ce Khartoum babban birnin kasar Sudan na da mutuware da ke daukar gawarwaki 150, amma ana da fiye da gawarwaki 3000 a yanzu. Babu wanda ya san ko su wane ne wadannan mutane saboda ana rufa-rufa game da musabbabin mutuwarsu.
A cewar jaridar dai, daruruwan mutane ne suka bace tun bayan fara juyin juya hali a karshen shekarar 2018. Dama da yawa sun bace tun bayan juyin mulkin shekara ta 2021. Wasu daga cikinsu suna gidan yari a garkame, yayin da mutane da yawa suka rigamu gidan gaskiya. Amma gano gawarwakinsu ba ya nufin an san sunansu da musabbabin mutuwarsu. Akwai mutane da yawa da ke son a ci gaba da wannan rufa-rufa saboda suna da hannu a wannan aika-aika. Yawancin gawarwakin sun shafe fiye da shekaru uku a mutuwaren birnin Khartoum. Wani masanin kimiyyar bincike hallita ya ce cututtuka na iya yaduwa tsakanin al'umma saboda warin gawarwaki ba ya a iya misaltuwa.
Jaridar ta ce Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango da ke tsakiyar Afirka dai na da matikar muhimmanci wajen kare halittu da tsirai. Ita dai Kwango ta kasance yanki na biyu mafi girma a cikin dazuzzuka a duniya bayan Amazoniya. Wannan ya sanya kasar da ke fama da talauci da yaki ya zama muhimmin ginshiki a shirin kiyaye dazuizzuka kan nan da shekarar 2030.