1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus sun yi magana kan #EndSARS

Zainab Mohammed Abubakar AS
October 23, 2020

A sharhunansu kan abubuwan da ke faruwa a Afirka, jaridun Jamus sun yi tsokaci kan zanga-zangar #EndSARS a najeriya da ma abin ya biyo baya.

https://p.dw.com/p/3kMOm
Nigeria Lagos | Protest EndSARS
Hoto: Adekunle Ajayi/NurPhoto/picture-alliance

A sharhin da ta rubuta, jaridar Neue Zürcher Zeitung ta maida hankali ne game da halin da ake ciki a Najeriya mai taken "Afkawa masu zanga zanga da karfin soji a Legas wand ata ce ya ''kara harzuka da jama'a da gwamnati". Jaridar ta cigaba da cewar hotunan bidiyo da ake yadawa a kafofin sada zumunta na nuni da yadda masu zanga-zangar suka ranta a na kare cikin fargaba, wasu na faduwa a kasa sannan an ji karar harbin bindigogi da ihun mutanen da ke kiran neman taimako.

Guinea Präsidentschaftswahl 2020 Conakry | Makalé Traoré
Ana fargabar samun tashin hankali baye zaben shugaban kasa a GiniHoto: Bangaly Condé/DW

Ita kuwa jaridar die Tageszeitung sharhi ta rubuta mai taken "Fargabar sabani kan zabe a Gini". Jaridar ta ce shugaban 'yan adawa Cellou Diallo ya ayyana kanshi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar Lahadi, wanda ke nuna da alamun rikici dangane da sakamakon zaben. Tun a ranar Litinin ce dai madugun adawar mai shekaru 68 da haihuwa ya ayyana nasarar a taron manema labaru da ya yi a birnin Conakry, fadar gwamnatin kasar ta Gini. Sai dai Diallo ya gaza bayar da cikakkiyar shaida da ke nuni da cewar shi ne ya ke da mafi yawan kuri'u.

Daga batun siyasa sai kuma matsalar amfani da kananan yara a gonakin Cocoa kasashen Cote 'd'ivoire da Ghana. Jaridar die Tageszeitung ta ce sakamakon wani binciken na nuni da cewar akalla yara kanana maza da mata miliyan daya da rabi ne wannan matsala ta shafa.

Elfenbeinküste | Junger Kakaoplantagenarbeiter in Guezon
Kungiyoyi na kokawa kan amfani da yara wajen noman koko a Ghana da Ivory CoastHoto: imago images/UIG/Godong

Binciken wata kungiya mai zaman kanta da ake kira Inkota Network da aka kafa tun a shekarar 1971, na nuni da yadda ake gallaza wa yaran a gonakin Cocoa kafin su kai ga wadanda ke jin dadin cinsa bayan an sarrafa shi zuwa Chakuleti. Kungiyar ta jaddada cewar, ya dace a ce masu sayen Chakuletin a Jamus alal misali suna sane da yiwuwar amfani da yara kanana kafin a wajen sarrafa cocoa kafin ya kai ga matsayin da yake. Binciken mai shafuka 300 da aka gabatar a cibiyar nazarin ra'ayoyi da ke jami'ar Chicago na nuni da cewar kashi 70 cikin da ke fitowa daga yankin yammacin Afirka, daga kasashen Ghana da Ivory Coast suke. Inda kuma ake tilasta yara maza da mata masu shekaru tsakanin 5 zuwa 17 aikin karfi, wanda kuma ke zama hadari ga rayuwarsu.