1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhuna kan kasashenmu na Afirka

Zainab Mohammed Abubakar
December 24, 2021

Tashe tashen hankula a yankin yammacin Afirka da zanga zangar adawa da mulkin soji a Sudan na daga cikin batutuwan da jaridun Jamus suka yi nazari.

https://p.dw.com/p/44oBh
Symbolbild deutsche Presseschau Presse
Hoto: picture-alliance/dpa

Zamu yaye kallabin sharhunan jaridun na Jamus na wannan makon ne da labarin da jaridar die Tagesteitung ta rubuta a kan ta'azzarar hare haren masu tarzoma a wasu kasashen Afirka mai taken "Tare kofarka daga makiyan da baka sani ba".

Jaridar ta ce bayan Mali da Nijar da Burkina Faso, a yanzu haka kasashen bakin ruwa na Benin da Togo da Cote d'voire na saran samun karin tasje tashen hankula na masu kaifin kishin addinin Islama.

Jamhuriyar Benin ta kasance cikin dimuwa a farkon watan Disamba, lokacin da aka kaiu hari a garin Porga da ke yankin Arewa maso Yammacin kasar kusa da kan iyakar Togo da Burkina Faso da yayi sanadiyyar rayukan jami'an sojoji guda biyu.

A kusa da garin ne kuma Benin din take da katafaren wurin shakatawa na kasa na Pendjari, wuri da ke zama na farkon inda masu yawon bude ido ke kai ziyara. A dai dai lokacin da ake bukukuwan kirsimeti, hari na zama abu mafi muni ga ci gaban kasar. Sanarwar rundunar sojin kasar na alakanta harin da wata kungiya da ke goyon bayan na masu jihadi da ke Mali. A daya bangaren kuma suna iya zama 'yan fashi ne kawai.

Tashe tashen hankula a Burkina Faso
Tashe tashen hankula a Burkina FasoHoto: Sophie Garcia/AP/picture alliance

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi tsokaci ne game da janyewar mayakan Tigray daga yankin arewacin kasar inda suke gwamza fada da dakarun gwamnati.

Jaridar ta ci gaba da cewar, mayakan neman 'yancin Tigray na TPLF na muradin bude kofa don a shigar da kayan agaji, a daya hannun kuma gwamnati na ayyana nasara a kan mayakan. Tun a ranar Litinin ne dai, mai magana da yawun mayakan na Tigray a shafinsa na Twitter ya sanar da cewar, sun kammala janye mayakansu daga gundumomin Amhara da Afar.

A cewar sanarwar dai, tuni kungiyar ta aikewa babban sakataren MDD Antonio Guterres wasikar tayin sasanci, da zarar an kawo karshen fadan. A baya dai mayakan na Tigray sun ki janyewa, bisa zargin mayakan gwamnati da kafiyar mamayen Amhara da Afar, batun da ya hana yiwuwar hawa teburin sulhu.

Tun daga watan Oktoba ne dai bangarorin biyu ke ikirarin nasara, a wannan yaki da ya dauki tsawon watanni 13 yana gudana. Yakin da ya haddasa asarar dubban rayuka daura da miliyoyi da suka tsere daga matsugunnensu a wannan kasa ta biyu mai mafi yawan al'umma bayan Najeriya, a kuriyar Afirka.

Mayakan Tigray
Mayakan TigrayHoto: S.Getu/DW

"An dauki firaministan Sudan a matsayin shahidi, a yanzu da dama na kallonsa a matsayin maci amana" wannan shi ne taken labarin jaridar Neue Zürcher Zeitung a kan halin da ake ciki a Sudan. Jaridar ta ce, a 'yan makonni kalilan da suka gabata ne masu zanga zanga ke dauke da kwalaye da hotunan wata fuska mai murmushi da gashin baki.

Fuskar framinista Abdallah Hamdok ne, masanin tattalin arziki da ya zama framinstan Sudan tun daga shekara ta 2019. A lokacin zanga zangar Hamdok yana daurin talala a gidanasa. Sojoji sun kifar da gwamnatin wucin gadi da ya ke shugabanta, wadda ita ce zata jagoranci kasar zuwa demokradiyya. A Khartoum da sauran manyan birane dai an ga dubban mutane sun shiga zanga zangar adawa da matakin sojojiin.

To sai dai a ranar Lahadin da ta gabata, Khartoum din da sauran birane 20 na Sudan sun gasabuwar zanga zanga. Sai dai a wannan karon lamarin ya rikide, babu hotunan Hamdok. Kasancewar Hamdok ya sake karbar mukamin framinista, kuma acewarsu ya ci amana. A ranar 21 ga watan Nuwamba ne dai, wadanda suka yi masa daurin talala suka sake rantsar da Hamdok mai shekaru 65 a matsayin framinista.

Masu zanga zanga a Sudan
Masu zanga zanga a SudanHoto: AFP/Getty Images

Yanzu haka yana jagorantar gwamnatin hadin gambizar sojoji da farar hula na wucin gadi. Sai dai masu zanga zangar sun ce sun yi hannun riga da wannan hadaka da sojoji.