Jaridun Jamus sun yi tir da sa yara aikin soji
September 27, 2019Jaridar Die Tageszeitung ta ce shirin wanzar da zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu ya ba da wani yanayi na shigar da kananan yara aikin soji inda dukkan bangarorin da ke yaki da juna ke kara yawan dakarunsu. Jaridar ta ce kamata ya yi a ce tuni an samu zaman lafiya a Sudan ta Kudu amma wanin binciken da Hukumar kare 'yancin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ya gano cewa kungiar 'yan tawaye da sojojin gwamnati na tilasta wa kananan yara daukar makami, yayin da wasu yaran ma don radin kansu suke shiga bangarorin da ke yakar juna. A cikin watan Nuwamba mai zuwa ya kamata shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir da tsoho mataimakinsa kuma jagoran 'yan tawaye a yanzu, Riek Machar sun kafa gwamnatin rikon kwarya da za ta kai ga samun hadin kan kasa, kamar yadda yarjejeniyar zaman lafiya ta watan Satumban 2018 ta tanada. Amma maimakon zaman lafiya ta samu sai bangarorin da ke rikici da juna suna amfani da wannan dama suna kara yawan sojojinsu musamman ma kananan yara.
Ebola ta yadu a Tanzaniya sakamakon sakacin mahukunta
An soki kasar Tanzaniya da rashin ba da cikakken hadin kai biyo bayan zargin bullar cutar Ebola, wannan shi ne taken sharhin da jaridar Der Tagesspiegel ta yi inda ta kara da cewa a ranar 8 ga watan nan na Satumba wata likita da ta yi balaguro a kasar Yuganda, ta rasu a birnin Dar Es Salam sakamakon wani zazzabi mai kama da cutar Ebola. Mutanen da suka yi hulda da likitar su ma sun kamu da rashin lafiya. Ko da yake mahukuntan kasar Tanzaniya sun ce ba wanda ya harbu da kwayar cutar Ebola. Amma Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce wasu rahotanni da ba na hukuma da ta samu a ranar 11 ga watan Satumba sun ce gwajin da aka yi likitar ya nuna ta kamu da Ebola. Sannan a ranar 12 ga Satumba WHO ta samu rahoton cewa an kwantar da wani dan shekara 27 asibiti a Dar Es Salam bisa zargin kamuwa da kwayar Ebola. Sai dai ma'aikatar kiwon lafiya ta Tanzaniya da ba ta taba yaki da barkewar Ebola ba ta musanta labarin. Ta kuma ki bukatar da WHO ta yi ta bincike a gwajin da ta yi duk da ka'idojin kiwon lafiya na duniya da suka tilasta yin haka. An dauki tsawon kwanaki hudu kafin mahukuntan Tanzaniya su mayar da martani ga bukatun WHO, duk da cewa tun wasu watanni ke nan a yankin kasashe makwabtan Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na cikin shirin ko ta kwana, inji jaridar. Ga shi kuma ana samun bullar cutar ta Ebola a wasu sabbin wurare a yankin.
Ana samun kwan-gaba kwan-baya da dokoki a kasar Senegal
Ita kuwa jaridar Neues Deutschland a wannan mako ta leka kasar Senegal ne tana mai cewa ci-gaban kasar ya tsaya ne a kan takarda, inda ta ruwaito kungiyoyi masu zaman kansu suna sukar gwamnati da rashin aiwatar da muradu masu dorewa da gwamnati ta shigar da su cikin tsare-tsarenta na kasa. Jaridar ta ce daga shekarar 2015 Senegal ta kafa wata doka da ta haramta amfani da jakukunan leda, to amma har yau ba a aiwatar da ita ba. A ranar 20 ga watan nan na Satumba wato fiye da shekaru hudu bayan kafa waccan doka, ministan kula da ci-gaba mai dorewa ya yi alkawarin kafa sabuwar dokar haramta amfani da jakukunan leda da za ta fara aiki a karshen shekara. To sai dai ganin yadda aka kasa aiwatar da dokar farko ta shekarar 2015, a wannan karon ana saka ayar tambaya ko mahukunatn kasar ta Senegal da gaske suke, domin har yanzu ana rashin wani sahihin mataki daga bangaren gwamnati na wayar da kan jama'a game da dokar da ke da nufin kare muhalli.