1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Tsamin dangantaka tsakanin Ruwanda da Faransa

Mohammad Nasiru Awal
December 2, 2016

Zargin da Ruwanda ke yi wa Faransa da hannu a kisan kare dangin 1994 da zaben Gambiya sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/2Te07
Ruanda - Präsident Paul Kagame
Hoto: DW/S. Karemera

Za mu fara sharhin jaridun na Jamus kan nahiyar ta Afirka da jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta fara da cewa neman mai laifi tana mai mayar da hankali da dangantaka da ta dade dea yin tsami tsakanin Ruwanda da Faransa da a cewar jaridar yanzu za ta kara yin muni bayan da lauyoyin gwamnatin Ruwanda suka fara binciken wasu Faransa 20 dangane da rawar da ake zargi sun taka a kisan kare dangi da ya auku a Ruwandar a shekarar 1994. Tsakanin watan Afrilu da Yulin 1994 mutane fiye da dubu 800 sojojin sakai na 'yan Hutu suka kashe a kasar. Gwamnatin Ruwandar ta yanzu ta kwashe tsawon shekaru tana zargin Faransa da laifi a kisan kare dangin. Gwamnati a Kigali ta ce akwai shaida cewa mahukuntan Paris sun tallafa wa gwamnati karkashin Hutu a bangarorin siyasa da soji kuma ta ci gaba da tura mata da makamai bayan an fara aikata kisan kare dangi duk da takunkuman Majalisar dinkin Duniya.

Maganin kashe kwari don fatattar aljannu

Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung a labarinta mai taken amfani da feshin maganin kashe kwari don korar aljannu ta fara da cewa malaman coci ko fastoci a Afirka ta Kudu na amfani da wasu dubaru na yaudara don nuna wa wadanda suka imani mu'ujirar Mahalicci.

Katholische Kirche in Juba
Hoto: Getty Images/AFP/Trevor Snapp

Jaridar ta ce daya daga cikin wadannan fastoci shi ne Prophet Lethebo Rabalago da ke amfani da maganin kashe kwarin  yana fesawa a fuskar masu halartar cocinsa yana mai ikirarin cewa zai iya magance ciwon ido da cutar daji ko kyansa da ma cutar HIV Aids ko Sida. Ya ce wahayi ya samu daga Ubangiji na amfani da maganin kashe kwarin kan al'ummarsa. Sai dai martanin da aka yi ta shafin Facebook ya nuna yadda 'yan Afirka ta Kudun suka fusata da matakin malamin cocin.

Yahya Jammeh na fuskantar adawa mai tsanani

A yayin da ake dakon sakamakon zaben shugaban kasar Gambiya da ya gudana a ranar Alhamis jaridar Die Tageszeitung tsokaci da cewa:

Shugaba Yahya Jammeh da tun a 1994 yake kan karagar mulki yake kuma kara zama wani shugaban kama karya ya dauki dukkan matakai don yin tazarce. To sai dai dan takarar gamaiyar jam'yyun adawa Adama Barrow na da kyakkyawar damar zama mutumin da zai kawo karshen mulkin shugaban na Gambiyar da ke son zama shugaba na dindindin.

Kame wani Basarake ya tada rigima a Yuganda

Uganda Polizei stellt Waffen von Rebellen sicher
Tarin makamai da 'yan sandar Yuganda suka kwace daga hannun 'yan tawayeHoto: DW/E. Lubega

Tashin hankali a Rwenzururu inji jaridar Süddeutsche Zeitung tana mai cewa gwamnati a birnin Kampala na kasar Yuganda ta bari an kame wani Basarake wanda kimanin shekaru bakwai da suka gabata gwamnati ta amince da masarautar ta gargajiya. Sai dai wasu daga cikin al'ummar yankin na bukatar samun 'yancin kansu daga Yuganda, abinda ya rika haddasa rikici a yankin, rikicin kuma da ya sake yin kamari yanzu. Hukumomi sun ce 'yan tawaye sun farma wani caji ofis, sun halaka jami'an 'yan sanda da yawa. Saboda haka a ranar Lahadi dakarun tsaro suka yi wa fadar basaraken dirar mikiya suka kame shi. Akalla mutane 60 aka kashe ciki har da magoya bayan sarki da kuma 'yan sanda.