1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Zabe cikin matsin tattalin arziki

Mohammad Nasiru Awal
December 9, 2016

Zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da aka gudanar a ranar Laraba a kasar Ghana da sanarwar shugaban Angola na yin bankwana da mulki a badi.

https://p.dw.com/p/2U2Hn
Ghana Wahlen
Hoto: Reuters/L. Gnago

A labarinta mai taken zabubbuka a lokacin matsin tattalin arziki da rashin aikin yi jaridar die Tageszeitung cewa ta yi.

Zaben kasar Ghana a wannan karon ya zo a daidai lokacin da kasar ke fama da koma-bayan tattalin arziki da matsalar rashin aikin yi tsakanin matasanta. Wadannan batutuwa da ma zargin mambobin gwamnati mai mulki da yawan cin hanci da rashawa sun dauki hankalin masu kada kuri'a a kasar ta Ghana. Sai dai akasarin 'yan kasar ba su da wata yarda ga shugabanninsu da ma jam'iyyun da suke wakilta. Yabo ta tabbata ga hukumar zabe da kuma al'ummar kasar bisa gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana ba da wani tashin hankali ba sabanin yadda aka saba gani a wasu kasashen Afirka.

Bankwana da shugabancin kasa bayan shekaru 37

Shugaba na dindin zai sauka, inji jaridar Neue Zürcher Zeitung sannan sai ta ci gaba tana mai cewa.

Bayan shekaru 37 a kan mulki, ba zato ba tsammani Shugaban Angola Jose Eduardo dos Santos ya bada sanarwar yin murabus a shekarar 2017. Shugaban mai shekaru 74 tun a 1979 ya karbi ragamar mulki. Ko da yake bai bada dalilin daukar wannan mataki ba amma an yada jita-jitar cewa yana fama da rashin lafiya. Sai dai jam'iyyar da ke jan ragamar mulki ta MPLA ta yi watsi da wannan labari inda ta yi kira ga 'yan Angola da su nesanta kansu daga karerayi na shafukan sada zumunta. Ana kyautata cewa 'yar shugaban Isabel da ke zama mace mafi arziki a nahiyar Afirka za ta gaji mahaifinta, amma wata majiya ta ruwaito shugabannin jam'iyyar MPLA na cewa ministan tsaro Joao Lourenco zai karbi ragamar mulki bayan Shugaba dos Santos ya sauka.

Gurfanar tsohon kwanmandan LRA gaban kotun ICC

Dogon jeri na mummunar ta'asa, wannan shi ne taken labarin da jaridar Süddeutsche ta rubuta dangane da gurfanar tsohon kwamandan kungiyar tawayen Lord's Resistance Army ta Yuganda Dominic Ongwen a gaban kotun hukunta manyan laifukan yaki ta kasa da kasa.

Ana zargin tsohon dan takifen da kisan kai, cin zarafin dan Adam da fyade da tilasta mutane yin aikin bauta a arewacin Yuganda daga shekarar 2002 zuwa 2005. Sai dai dai ya musanta aikata wadannan laifuka yana mai cewa kungiyar ta LRA ta aikata. Tun yana yaro dan shekara 10 zuwa 14 kungiyar ta yi garkuwa da shi ta tilasta masa shiga aikin soja. Kasancewa shi ma an ci zarafinsa lauyansa ya roki kotun da ta yafe masa.

Kisan kare dangi a Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da kisan kare dangi a Sudan ta Kudu har wayau dai iji jaridar Süddeutsche Zeitung.

Ta ce masu sanya ido kan al'amuran yau da kullum na zargin sojojin sa kai na amfani da yi wa mata fyade cikin gungu, a matsayin makamin tursasa wa wasu kabilu suna tilasta musu barin yankunansu na asali. Jaridar ta ce yanzu haka dubun dubatan mutane sun tsere zuwa kasashe makotan Sudan ta Kudun.