1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin Angela Merkel a majalisa kan batun neman mafaka

Salissou BoukariOctober 15, 2015

A wani mataki na neman samun tsari na bai daya kan masu neman mafaka tsakanin kasashen Turai Shugabar gwamnatin Jamus ta gabatar da jawabi a majalisar dokokin kasar.

https://p.dw.com/p/1GovL
Angela Merkel
Angela MerkelHoto: Reuters/H. Hanschke

Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta kuma nemi samun matsaya kan tsaurara dokoki na samun mafaka, inda wadanda ba su cancanta ba za a tisa keyarsu daga Jamus, amma wadanda suke bukatar kariya za su samu taimako. Akwai yuwuwar majalisar dokokin kasar ta Bundestag ta kada kuri'ar rashin amincewa da dokar tallafin 'yan gudun hijira. Sai dai shugabar gwamnatin Merkel ta bukaci wakilan majalisa da su amince da ayar dokar:

Merkel ta nemi da a amince da dokar

"Ina bayyana mahimman abubuwa da shirin doka ya tanada. Hakkin gwamnatin tarayyar ne wajen bayar da taimakon kudade ga jihohi da al'umomi."

Angela Merkel
Angela MerkelHoto: Reuters/H. Hanschke

Merkel ta kara da cewa karkashin shirin za a kara gina gidajen marasa galihu, da kula da yara wadanda ba su iso kasar tare da iyaye ba. Za kuma a kara hanzari wajen tantance takardun masu neman mafaka. Sannan wani abu mai mahimmanci karkashin dokar za a bayyana kasashen Albaniya, da Kosovo gami da Montenegro a matsayin kasashe marasa hadari, saboda a yi watsi da takardun 'yan kasashen masu neman mafaka. Jawabin ya zo ne gabani tafiyar da Merkel za ta yi zuwa birnin Brussels na kasar Beljiyam, wajen taron kungiyar Tarayyar Turai, inda ta jaddada matsayin kare mutanen da suka fito daga kasashen da ake samun tashe-tashen hankula:

"Wadanda suka tsere wa yaki da tsangwama duk za su samu taimakon da ya dace daga wajen mu."

Deutschland Pegida Kundgebung in Dresden
Hoto: Reuters/H. Hanschke

Masu adawa da wannan tsari na sukarsa

Kungiyoyin jinkai gami da masu bincike kan hijira na mutane sun yi suka kan matakin. Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta kuma nemi kasashen Turai su yi aiki da kasar Turkiya wajen dakile matsalar 'yan gudun hijira. Saboda mahimmancin kasar ta Turkiya, a karshen mako Merkel ta yi bulaguro zuwa kasar. Akwai kimanin 'yan gudun hijira milyan biyu daga Siriya wadanda suke kasar ta Turkiya, kuma galibin wadanda suke shiga Jamus a matsayin 'yan gudun hijira an hakikance cewa sun fito ne daga kasar ta Siriya, da sauran wuraren da ake samun tashe-tashen hankula a Gabas ta Tsakiya da Afirka musamman kudu da Sahara.