1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin Merkel ga majalisar wakilan Amirka

November 4, 2009

Angela Merkel ta kasance wata shugabar gwamnatin Jamus ta farko da ta yi jawabi gaban majalisar dokokin Amirka bayan Konrad Adenauer a shekara ta 1957

https://p.dw.com/p/KOYj
Shugabar gwamnati Angela Merkel gaban majalisar dokokin AmirkaHoto: AP

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, wadda ta fara ganawa da shugaba Barak Obama na Amirka gabannin yiwa zaman haɗin gwiwar majalisun dokokin ƙasar jawabi - a dai dai lokacin da ƙasarta ke shirye shiryen gudanar da shagulgular cika shekaru ashirin da faɗuwar katangar Berlin - katangar da a baya ta rabe tsakanin gabashi da kuma yammacin Jamus, ta miƙa godiyarta ga Amirka bisa rawar data taka wajen haɗewar yankunan biyu:

Merkel vor dem Kongress in Washington
Merkel a majalisar dokokin AmirkaHoto: AP

" Ina so ku bani dama in nuna cewar mu Jamusawa muna sane da irin abubuwan da ku, abokan mu Amerikawa kuka yi mana. Har abada ni kaina musamman ba zan taɓa mantawa da hakan ba."

Jawabin na Merkel, ya kuma taɓo batun dunƙulewar duniya wuri guda, game da buƙatar yin saiki tare:

" Har a wnanan lokaci, cikin ƙarni na 21, kuma a zamanin da duniya ta zama gida ɗaya; al'umma ɗaya, babu abin da ba za'a iya aiwatar dashi ba. A can gida a Jamus da kuma a nan gaba ɗaya mun san cewar batun maida duniya ƙauye ɗaya, abune dake kawo damuwa da tsoro a zuƙatan jama'a. Wannan kuwa hali ne da ba zamu yi watsi dashi ba. Muna sane da wahalolin dake akwai, to amma alhakin mu ne mu ja hankalin jama'a, mu nuna masu cewar ƙoƙarin maida duiya ta zama ƙauye ɗaya, wata babbar dama ce ga ko wace nahiya. Saboda hakan zai tilastawa duka kasashe su haɗa gwiwa su riƙa yin komai tare. Rashin samun wannan haɗin kai babu abin da zai haddasa, illa koma baya, ƙaruwar talauci da kuma maida kasashe su zama saniyar-ware. Muna sane da cewar Turai da Amerika ba ko wane lokacine suke da ra'ayoyi iri ɗaya ba. Wani lokaci mu kan zargi junan mu da laifin tsoro ko jan kafa a wasu al'amura, to amma nayi imanin cewar babu wata ƙawa da ta dace da Turai fiye da Amerika, babu wata ƙawa da ta dace da Amerika irin Turai."

Data juya ga fafutukar yaƙi da masu tada tarzoma kuwa, Merkel ta ce, Jamus ta ƙuduri anniyar yin aiki kafaɗa da kafaɗa da Amirka a wannan fannin ma:

" Muna iyakacin ƙoƙarin mu a matakan yaƙi da aiyukan tarzoma a duniya baki ɗaya. Muna kuma sane da cewar babu wata ƙasa, komai ƙarfin ta da zata sami nasarar wannan yaƙi ita kaɗai. Dukkan mu gaba ɗaya muna buƙatar abokan haɗin gwiwa, inda sai tare da wannan haɗin kai ne zamu nuna ƙarfin mu. Saboda haka ne a bayan hare-haren ranar 11 ga watan Satumba, muka daidaita tare da tsohon shugaban Amerika, George Bush cewar nan gaba, ba zamu sake yarda Afghanistan ta ta zama cibiyar da zata haddasa haɗari ga tsaro da zaman lafiyar duniya ba. Jamus saboda haka ta kasance ƙasa ta ukku da suka fi yawan sojoji a ƙasar ta Afghanistan. Burin mu shine ganin matakan soja da na farar hula sun kai ga samun nasarar hana aiyukan tarzoma daga ƙasar ta Afghanistan. Babu shakka aiyukan da rundunar ƙasashen duniya take yi a Afghanistan suna da tsanani, to amma da zaran sabuwar gwamnatin da aka zaɓa a ƙasar ta kama mulki, wajibi ne a aiwatar da sabuwar manufar da zamu tsara. Manufar wannan shiri ita ce ɓullo da wani tsari inda 'yan Afghanistan sannu a hankali zasu sami ƙarfi aiyukan tafiyar da mulki da tsaron ƙasar su da kansu. Wannan tsari kuwa zamu shimfiɗa shi ne a lokacin wani wani taro na Majalisar Ɗinkin Duniya a farkon shekara mai zuwa. Ba kuwa zamu sami nasarar aiwatar da shirin ba, sai idan mun haɗa gwiwa a ko wane mataki zamu dauka. Jamus ba zata kaucewa ɗaukar wannan nauyi ba."

Kongress auf Capitol Hill Washington
Majalisar dokokin Amirka a Washington D.C.Hoto: AP

Merkel, ta kuma yaba da rawar da Amirka ke takawa wajen shawo kan matsalar ɗumamar yanayi a duniya:

" Ina farin cikin ganin cewar shugaba Obama da ku kanku a aiyukan ku, kuna bada muhimmanci ga matakan kare kewayen ɗan Adam. Gaba ɗaya muna sane da cewar bamu da sauran lokacin da zamu ɓata. Muna buƙatar daidaituwa kan batun kare muhalli a lokacin taron da za'a yi a Copenhagen a watan Disamba. Burin mu shine ganin an rage ɗumamar yanayin sararin samaniya. Samun nasarar haka yana buƙatar haɗin kan mu gaba ɗaya da cika alƙawura idan aka yi su. Kaucewa duk wani ƙoƙari na cika wannan buri ba abu ne da zai dace ba a ƙoƙarin kare muhallin mu. Muna buƙatar ɓullo da sabbin fasahohi, waɗanda zasu iya zama wata babbar dama ta samun bunƙasar tattalin arziƙin mu da kare wuraren aikin yi."

A wannan larabar ce dai, Merkel ke kammala wannan ziyarar ta yini biyu a ƙasar ta Amirka.

Mwallafi: Umar Saleh

Ediwa: Umaru Aliyu