Merkel Krise
October 8, 2008Ana ƙara nuna shakku kan yadda za'a magance wannan matsala wadda ke cigaba da dakushe bankunan duk da ƙokarin da ake na ceto su.
Ta ce: "Rikicin da kasuwar Amirka ta shiga ciki ya zama ruwan dare gama duniya. Ana iya cewar yanzu martabar harkokin kuɗi mafiya muhinmanci ta zube a idanun jama´a. Harta bankunnan da suke da ƙarfi so sai abin ya shafe su ma bankunan nan Jamus basu tsira ba. Shi ya sa ya zama wajibi a maido da yarda a cikin harkokin bankuna."
Amma kuma game da hanyoyin da zata maido da wannan yarda dole ne ta kare manufofin gwamnatinta, musanman ma batun ceto Bankin Hypo da aka yi kwanakin nan. Ta ce in da ba a´a dauki mataki cikin gaggawa ba da an samu wani munmunan sakamako ga bankunan Jamus da kuma sauran cibiyoyin kuɗi na ƙasashen turai. Bisa la'akari da abubuwan da ke tafe shugabar gwamnatin ta yi ammana cewar za'a samu masalaha nan ba da daɗewa ba. To sai dai Merkel ta soki ƙasar Ireland saboda ta yi gaban kanta, inda ta bada tabbaci ga dukkan bankunan ƙasar ta. Merkel ta bayyana wannan mataki na gurɓata ƙasuwa cewa wani abu ne wanda ba za'a amince da shi ba. Shugabar ta kawar da yiwuwar bada tabbaci na bai ɗaya tsakanin ƙasashen Turai, maimakon haka, sai ta gabatar da buƙatar cewar ƙasashe zasu iya taimakawa bankunansu idan durƙushewarsu za ta yi barazana ga tsarin gabaki ɗaya. Merkel ta fito fili ta amsa cewar daga bangaren gwamnati ma an yi wasu kurakurai. Tana mai yin kira da a yiwa shirin kula da harkokin kudi gyaran fuska. A dai dai wannan lokacin ne shugaban jamIyyar FDP mai sausaucin ra'ayi Guido Westerwelle ya yi tsokaci inda ya zargi gwamnati saboda rashin yarda da shugabar ta yi gargaɗi akai.
Yace: "Ana wasa ne da hankalin mutane idan aka ƙi fitowa fili a fadi gaskiyar maganar, irin wannan mataki ya barmu cikin duhu game da irin abinda gwamnati ta sani bisa halin da ake ciki. Amma abin da muka sani shine gwamnati ta gaza wajen kula da ayyukan bankuna."
Shugaban jam'iyar ´yan ra'ayin canji Oskar Lafontain ya yi amman cewar rikicin kuɗin ya yaɗu zuwa sauran harkokin tattalin arziki.
Kampanoni ƙera motoci masu yawa sun bada sanarwa rage yawan motocin da suke ƙerawa kuma zasu rage ma'aikata wanda ke haka ke nuni da tasirin wannan matsala a cikin tattalin arzikin ƙasa fiye da yadda ake tsammani.