1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin Olesegun Obasanjo a Hukumar Tarayya Afrika

October 10, 2006
https://p.dw.com/p/BugH

Shugaba Olesegun Obasanjo, na Tarayya Nigeria, ya gabatar da kakkaussan jawabi, a birnin Addis Ababa, na ƙasar Ehtiopia, a game da halin da ake ciki a yankin Darfur na ƙasar Sudan.

Obasanjo, ya kira ga hukumomin Khartum su amince da tayin Majalisar Ɗinkin Dunia, na aika dakaru a wannan yanki, da ke fama da tashe-tashen hankulla.

Ya ce matakin da Sudan ta ɗauka, ba mutunci ba ne,a gare ta, da ma Afrika da ma Afrika baki ɗaya.

Bai kamata ba,a zuba iddo, su na kallon dubunan jama´a na mutuwa, kokuma su na fama cikin matsalolin da a ke iya magancewa, da zaran gwamnatin Sudan ta bada haɗin kai inji Olesegun Obasanjo.

A ɗaya hannun, shugaban Nigeria, ya buƙaci ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, su matsa ƙaimi ga sauran ƙungiyoyin tawayen Sudan,, da ba su rattaba hannu ba, a kann yarjejeniyar zaman lahia.