1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin Putin na farko bayan boren Wagner

June 26, 2023

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi bayyanarsa ta farko tun bayan kawo karshen boren sa'o'i 24 na sojojin haya na Wagner.

https://p.dw.com/p/4T56y
Shugaba Putin na Rasha yayin da yake jawabi ta kafar talabijin din gwamnati
Shugaba Putin na Rasha yayin da yake jawabi ta kafar talabijin din gwamnatiHoto: Kremlin.ru/Handout/REUTERS

A wannan Litinin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya isar da sako ta kafar talabijin wa mahalarta wani taro da kasar ta shirya kan gudunmowar matasa wajen bunkasa mana'antu.

Sai dai a jawabin na sa shugaba Putin ya kauda kai kan boren da dakarun Wagner karkashin Evguéni Prigojine suka yi masa inda ya mayar da hankali kan barazanar durkushewa da mana'antun kasar ke fuskanta sakamakon takunkuman kashashen Yamma.

A daya gefe kuma shugaban kasar Iran Ebrahim Raïssi  ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa mista Poutin inda ya jaddada masa goyon baya a kan makarkashiyar da ake kokarin kitsa masa. Baya ga shugaban Iran, shugaban China da sarkin Qatar dukanninsu sun karkafa wa Putin guwiwa kan rikicin cikin gidan da kasar ta kusa fadawa a ranar Asabar 24 ga watan Juni, lamarin da ya girgiza fadar Kremlin da kasashen da take mu'amala da su.