1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin ayyana yankunan Ukraine cikin Rasha

Abdoulaye Mamane Amadou ATB
September 30, 2022

Fadar mulki ta Kremlin na shirin gudanar da wani kasaitaccen biki da zai ayyana shigar da yankunan Ukraine hudu da aka gudanar da zaben raba gardama cikinsu, cikin kasar Rasha.

https://p.dw.com/p/4HZJR
Russland | Zeremonie zur Annexion ukrainischer Gebiete | Putin mit den Besatzungschefs
Hoto: Grigory Sysoyev/AP Photo/picture alliance

Tuni birnin Moscow ya dau haramin shagulgulan bikin, wanda a cikinsa shugaba Vladimir Poutin zai gabatar da wani kasaitaccen jawabi mai kumshe da batutuwa masu muhimmanci, in ji kakakin fadar gwamnatin Rasha Dmitri Peskov.

Rahotanni na cewa tuni Rashar ta kaddamar da wakilian gwamnatinta a yankunan Donetsk da Lougansk da Zaporijjia da Kherson da ta mamaye a Ukraine tun a ranar Alhamis, bayan tabbatar da sakamakon zaben na Raba gardama.

Kasashen yammacin duniya da dama sun yi Allah wadarai da matakin Rasha na hade yankunan a matsayin nata, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi kakkausar suka kan matakin tare da bayyana shi a matsayin wanda bai da gurbi a wannan zamani.

A nata bangare Ukraine ta bukaci kwamitin sulhu na MDD da ya yi wani zaman gaggawa a yau don duba batun.