Jawabin shugaban ƙasar Iran Mahmoud Ahmedinejad
August 29, 2006Shugaba Mahmoud Ahmedinejad yace ya ƙalubalanci Bush da ya fito su yi muhawara a gaban jamaá ta akwatunan Talabijin a game da siyasar duniya domin baiyanawa jamaá zahirin gaskiyar lamura amma ba hauragiya ba. Yace ya kamata muhawarar ta kasance ƙarara kuma kai tsaye ba tare da yankewa ba domin baiwa Amurkawa damar sanin gaskiyar alámura yadda suke. Yace bunƙasa makamashin nukiliya ta hanyar lumana yanci ne na ƙasar Iran.
Mahmoud Ahmedinejad wanda ya yi jawabi ga taron manema labarai yace bisa laákari da ƙaídoji na ƙasa da ƙasa, Iran ta zabi hanya mafi dacewa ta bunƙasa makamashin ta domin samar da wutar lantarki ga jamaár ta, kuma babu wanda ya isa ya hana ta.
Ahmedinejad yace Iran ta zaiyana jadawalin tattaunawa a amsar da ta bayar ga tayin Ihsanin da manyan ƙasashe shida na duniya suka gabatar mata idan ta dakatar da shirin bunƙasa makamashin nukiliyar. Yace jadawalin ya ƙunshi mangartan matakai ta sulhunta taƙaddamar nukiliyar.
Bayanan na Ahmedinejad sun zo ne a daidai lokacin da waádin da Majalisar dinkin duniya ta debar masa na dakatar da shirin nukiliyar ke ƙara gabatowa. Kwamitin sulhun ya baiwa Iran nan da ranar Alhamis mai zuwa ta dakatar da shirin ɗungurunrum ko kuma ta fuskanci yiwuwar sanya mata takunkumi.
Ahmedinejad ya kuma yi shakulatin bangaro da kalaman jakadan Amurka a Majalisar ɗinkin duniya John Bolto ta neman a ƙaƙabawa Iran takunkumin karya tattalin arziki idan ta ƙi dakatar da shirin nukiliyar. Shugaban na Iran ya kuma yi tofin Allah tsine ga Amurka da Britaniya a game da rawar da suke takawa tun bayan yaƙin duniya na biyu.
Yace Amurka da ƙasashen Turai sune ke buƙatar amincewar ƙasashen duniya, yace a ko ina a duniya ana yi musu mummunan kallo ta rashin yarda. Yace a dai dai lokacin da ake ta yiwa alúmar ƙasar Lebanon hadarin bama bamai, abin ban haushi, abin takaici sun yi ta adawa da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, amma kai tsaye suka nemi a zartar da ƙudiri a kan mu. Wannan dai abin mamaki ne.
A waje guda kuma fadar White House ta yi fatali da kiran shugaban ƙasar Iran ɗin ta yin muhawara ta akwatin Talabijin da shugaba Bush. Sanarwar fadar ta White House, ta ce kiran gudanar da muhawarar wata hikima ce kawai ta kaucewa damuwar da duniya ke da ita a game da halaiyar Iran ta daurewa ayyukan taáddanci gindi da kuma burin ta na ƙera makamin ƙare dangi.
Mahmoud Ahmedinejad ya ƙara da cewa mun sha baiyana cewa ko yaushe a shirye muke mu shiga shawarwari da ko wanene ma, kuma mun ce a ranar 31 ga watan Augusta ne za mu baiyana shawarar da muka yanke, amma kwananaki goma kafin hakan, sun riga sun yanke shawara kan ƙudirin da suke niyyar zartarwa.
Ahmedinejad yace suna muámala damu tamkar bayin su, a saboda haka ina yi musu gargaɗi da su yi watsi da wannan salon da suke bi, kuma su sake halayen su da suke nuna mana.
A game da maida hulɗar jakadanci tsakanin Iran da Amurka, shugaba Ahmedinejad yace ai dama can Amurka ce ta katse dangantaka da Iran bayan juyin juya halin Islama a shekarar 1979, a saboda haka yace Idan Amurka na fatan maida hulɗar jakadancin to ita ce zata fara ɗaukar matakan yin hakan.
Ko da yake Mahmoud Ahmedinejad ba shi ne kat mai faɗa a ji ba a ƙasar Iran, kalaman sa sun sami karɓuwa matuƙa gaya wajen jagoran addini na ƙasar Ayatollah Ali Khameni.
Batun nukiliyar Iran ɗin dai ya haifar da rarrabuwar kawuna a kwamitin sulhun majalisar ɗinkin duniya, inda ƙasashen Amurka da Britaniya da kuma Faransa ke ƙoƙarin ganin an sanyawa Iran takunkumi, a waje guda kuma ƙasashen China da Rasha waɗanda ke da hulɗar cinikayya da Iran suke sukar lamirin wannan mataki.