Jeroen Dijsselbloem ya sake zama shugaban Eurogroup
July 13, 2015Talla
A wata sanarawa ce dai da jagororin na Turai suka fitar da yammacin wannan Litinin din, suka tabbatar da wannan zabe wanda hakan zai sake bashi damar jagorancin wannan gungu na ministocin kasashen masu amfani da kudadan Euro na tsawon wasu shekaru biyu da rabi nan gaba, gungun da a cikinsa kasashen ke kokarin kawo sauyi kan siyasar tattalin arzikinsu. Abokin hamayyar na Dijsselbloem wanda bai yi nasara ba, shi ne ministan kudin kasar Spain Luis de Guindos. A yanzu haka dai wannan tsari na Eurogroup na a matsayin wani dandalin da a cikinsa a ke tattauna batun matsalar tattalin arzikin kasar Girka wadda ta dauki hankalin kasashen na Turai.