1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban kasar China ya rasu

Abdourahamane Hassane
November 30, 2022

Tsohon shugaban kasar china Jiang Zemin, wanda ya jagoranci kasarsa a zamanin da aka yi fama da tashe-tashen hankula tun daga shekara ta 1989 zuwa farkon shekarun 2000, ya rasu yana da shekaru 96 a duniya.

https://p.dw.com/p/4KII3
China Jiang Zemin gestorben
Hoto: XINHUA/AFP

Jiang Zemin ya hau kan karagar mulki a jajibirin da aka kaddamar da yunkurin murkushe zanga-zangar da aka yi a dandalin Tiananmen na birnin Beijing, kuma ya kasance mutumin da ya jagoranci rikidewar kasar da ta fi yawan al'umma a duniya zuwa kasa mafi karfin tattalin arziki ya mutu sakamakon cutar sankara da kuma gazawar wasu sassan jikinsa a birnin Shanghai.