1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya na sukar matakin Amirka na kara jibge sojoji

Abdoulaye Mamane Amadou
June 18, 2019

Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martani da ma sukar matakin kasar Amirka na kara adadin bataliyar sojojinta da dubu daya a yankin Gabas Ta Tsakiya don fuskantar barazanar kasar Iran.

https://p.dw.com/p/3Kd43
Nord-Mazedonien gemeinsame Militärübung mit US Soldaten
Hoto: Getty Images/AFP/R. Atanasovski

Kasar Amirka ta bayyana anniyarta na kara jibge karin adadin sojojinta dubu daya(1000) a yankin Gabas Ta Tsakiya, tare da kira ga kasashen duniya da su jajirce wa sabuwar barazanar da kasar Iran ke nuna wa da makamashin Nukilyarta.

Patrick Shanahan wani jago a hukumar tsaron kasar Amirka ta Pentagone, ya ce binciken da ma'aikatar tsaron kasar ta gudanar ya tabbatar da cewar kasar Iran ce ta kai farmaki ga tankokin jiragen mai a tekun Oman, saboda hakan ba za su bari barazanar kasar Iran ta ci gaba da dorewa ba.

Sai dai tuni manyan kasashen duniya suke ci gaba da sukar matakin Amirka na kara adadin sojojin kasar dubu daya zuwa yankin na Gabas Ta Tsakiya suna masu kira ga bangarorin biyu da su sulhunta rikicin a cikin ruwan sanyi. 

Wannan matakin na Amirka na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Iran ta yi barazanar kara adadin makamashin Nukiliyarta daga Kilogram 300 zuwa sama kan nan zuwa wasu kwanaki 10 da ke tafe, adadin da ya zarta kima ga jarjejeniyar kasa da kasa da Iran din ta sanya hannu akai da kasashen duniya a shekarar 2015.

Kungiyar Tarayyar Turai ta EU, har yanzu tana ci gaba da nuna dari-dari game da takkadamar da ke dada zafi tsakanin kasar Amirka da Iran, inda a baya bayan nan ma Shugaba Emmaneul Macron na Fransa ya yi kira ga kasar Iran da ta kasance mai juriya da hakuri.