1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jigon al-Shabaab ya koma bangaren gwamnatin

August 13, 2017

Daya daga cikin manyan jiga-jigan kungiyar tsagerun al-Shabaab Mukhtar Robow Abu Mansur ya koma bangaren gwamnatin Somaliya.

https://p.dw.com/p/2i93u
Somalische Kämpfer sollen Al Kaida-Ableger im Jemen verstärken
Hoto: picture-alliance/dpa

Daya daga cikin jiga-jigan kungiyar tsageru ta Al-Shabaab da ke Somaliya, Mukhtar Robow Abu Mansur ya koma bangaren gwamnati kamar yadda wani jami'in soja ya tabbatar.

Shi dai Robow Abu Mansur ya kasance tsohon mataimakin shugaba kana mai magana da yawun kungiyar a shekara ta 2013. Yanzu haka Robow Abu Mansur yana garin Hudur inda wani jirgin sama zai kai shi birnin Mogadishu fadar gwamnatin Somaliya. Kafin ya koma bangaren gwamnatin Somaliya mahukuntan Amirka sun cire sunansa daga cikin wadanda ake nema ruwan a jallo a mace ko a raye.

Gwamnatin Somaliya da taimakon dakarun kiyaye zaman lafiya na Afirka sun kwace galibin yankunan da ke hannun tsagerun na kungiyar al-Shabaab masu nasaba da al-Qaeda.