1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump zai iya hana jarirai zama 'yan Amurka kai tsaye?

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim AH
January 22, 2025

Jihohi 22 na jam'iyyar Democrats da wasu kungiyoyin kare hakkin bil'adama, sun kalubalanci Shugaba Donald Trump kan janye 'yancin zama dan kasa kai tsaye ga yaran da aka haifa wandanda iyayensu ba su da cikakkun takaurdu

https://p.dw.com/p/4pSC5
Shugaban Amurka, Donald TrumpHoto: Jim Watson/AFP/Getty Images

Sauran wadanda suka shiga cikin hadin gwiwar shigar da karar a kotu, sun hada da gundumar Colombia da kuma birnin San Francisco, domin nuna adawa da matakin Mr Tump na haramta wa jarirai sama da dubu 150,000 da a ke haifa a Amurka duk shekara samun izinin zama 'yan kasa, duk kuwa da cewa iyayensu bakin haure ne da kuma 'yan gudun hijira.

Matakin soke izinin zama dan kasa da Donald Trump ya yi ga yaran da iyayensu ke shiga kasar ba bisa ka'ida ba, na daya daga cikin kudurodin da shugaban ya yi alkawarin tabbatarwa da zarar ya sake hayewa kan karagar mulki a zangon mulkinsa na biyu.

Shugaba Trump ya saka hannu kan dokokoki da dama ciki har da janye Amurka daga hukumar lafiya ta duniya WHO da kuma yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, lamarin da ya janyo muhawara daga ciki da wajen kasar.