Jimami a Somaliya bayan harin ta'addanci
March 22, 2018Talla
Mahukuntan kasar ta Somaliya dai sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike domin gano sauran wadanda harin da aka kai a kusa da Otal din Weheliye da ke kan titin Makka Almukarramah a Mogadishu babban birnin kasar ya rutsa da su. Dama dai hanyar ta kasance wadda ke yawan fuskantar hare-haren ta'addanci daga kungiyar masu kaifin kishin addini ta al-Shabab da ke zaman mafi hadari a nahiyar Afirka, wadda kuma ta addabi Somaliyan. Tuni ma dai kungiyar ta al-Shabab ta dauki alhakin kai wannan harin.