Aleppo: An sami tsaikon kwashe fararen hula
December 14, 2016Bayanai daga Siriya na cewa an sami tsaiko wajen kwashe jama’a fararen hula daga gabashin Aleppo, sai dai yan adawa sun zargi gwamnati da haddasa jinkirin.
Yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi da aka cimma tsakanin yan tawaye da gwamnatin Assad ta cigaba har izuwa safiyar wannan Laraba. Yarjejeniyar dai ta biyo bayan tattaunawa ce tsakanin Rasha babbar mai marawa Assad baya.
Ficewar da ake sa ran mayakan yan tawaye za su yi daga gabashin Aleppo wata alama ce ta babbar nasara da shugaban Siriya Bashar Al Assad ke fatan gani bayan kwashe fiye da shekaru biyar ana yakin basasa.
Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vitaly Churkin ya shaidawa kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya a daren ranar Talata cewa an tsagaita bude wuta a gabashin Aleppo kuma gwamnatin Siriya na rike da cikakken ikon gabashin yankin.
A matakin saranda, mayakan yan tawaye da iyalansu za su fara janyewa daga bakin da-ga a Aleppon yayin da sojojin Assad kuma ke dannawa birnin a bangare guda.