1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jiragen Siriya sun ci gaba da luguden wuta

Abdullahi Tanko Bala
January 2, 2017

Ci gaba da luguden wuta na jiragen yakin Siriya na yin barazana ga yarjejeniyar sulhu da ke tangal tangal wadda Rasha da Turkiyya suka cimma a makon da ya gabata.

https://p.dw.com/p/2V808
Syrien Assad Regime verletzt Waffenruhe in Aleppo
Hoto: picture alliance/dpa/AA/A. al Ahmed

Jiragen yakin Siriya sun ci gaba da luguden wuta a kan yankin 'yan tawaye a Wadi Barada da ke arewa maso yammacin Damascus bayan tsaikon hare haren na tsawon sa'o'i 24 a ranar Lahadi a cewar wani jami'i na 'yan tawayen da kuma kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil Adama a Siriya.

'Yan tawayen sun yi barazanar yin fatali da yarjejeniyar tsagaita wutar da Rasha da Turkiyya suka cimma wadda ta fara aiki a ranar Juma'ar da ta wuce idan gwamnatin da kawayenta suka ci gaba da saba yarjejeniyar.

Kungiyar sa ido kan kare hakkin bil Adama a Siriya da kuma wasu majiyoyin soji a Damascus sun ce daruruwan fararen hula sun fice daga garin na Wadi Barada.