Jiragen yaki na ci gaba da barin wuta a Aleppo
September 26, 2016Talla
Rahotanni da ke samun tushe daga mazauna birnin na Aleppo, na cewar wasu jiragen yaki da ake zargin na dakarun da ke yin biyayya ga gwamnatin Siriya ne ke ci gaba da yin lugujen wuta a yankin wanda ya yi sanadiyyar barnata wuraren samun ruwan sha da sauran gine-gine masu mahimmanci a yankin.
Masu aiko da rahotanni dai sun ce sabon harin ya yi sanadiyyar rayuka da dama ciki har da 'yan tawaye da fararen hula, a ranar 12 ga watan Satumba ne kashen Rasha da Amirka suka cimma yarjejenyiar tsagaita wuta akasar. To amma bude wuta a kan ayarin Majalisa Dinkin Duniya da ke kai kayan agaji a farkon makon cimma yarjejenyar ne ya kawo karshen tsammanin samun zaman lafiya a kasar ta Siriya.