Jiragen yakin Amirka sun kai babban hari a Pakistan
July 3, 2013Wani harin da jiragen saman yakin Amirka - marasa matuka suka kaddamar a kusa da iyakar kasar Pakistan ya haddasa mutuwar akalla mutane 16. Jami'an tsaron da suka bayyana cewar da sanyin safiyar wannan Larabar ce jiragen yakin suka kaddamar da harin, sun kara da cewar, makamai masu linzami biyu ne da suka fada akan wani gidan da ke kusa wata babbar kasuwar Miranshah, wanda ke zama cibiyar lardin arewacin Waziristan. Sai dai kuma ya zuwa yanzu ba a san mutanen da harin ya rutsa da su ba. Wannan harin dai shi ne mafi girman da kasar Amirka ta kaddamar a Pakistan cikin wannan shekarar, kana shi ne na biyu tun bayan da Nawaz Sherif ya dare bisa kujerar firaministan kasar ta Pakistan, bayan nasarar da ya samu a zabukan kasar da suka gudana cikin watan Mayu. Dama dai Sherif ya bukaci Amirka ta daina kai hare-hare ta jiragen saman yaki - marasa matuka, bisa dalilin cewar, sun keta 'yancin zaman Pakistan a matsayin kasa.
Mawallafi : Saleh Umr Saleh
Edita : Umaru Aliyu