Jiragen yakin Siriya sun hallaka farar hula 25
April 23, 2016A Siriya fararan hula 25 sun mutu a wannan Asabar a cikin wani sabon harin da jiragen yakin gwamantin Bashar al-Assad suka kaddamar a biranen Alepo da Douma.
Daraktan kawancan kungiyoyin kare hakkin bil Adama na kasar ta Siriya wato OSDH Rami Abdel Rahmane, ya ce a halin yanzu za a iya cewar yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin 'yan tawayen da gwamnati a karakshin jagorancin kasashen Amirka da Rasha a ranar 27 ga watan Febraru ta wargaje, bayan da ko wani bangare ya koma keta haddin yarjejeniyar ta hanyar harar abokin gabarsa.
Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewar hare-haren jiragen yakin na wannan Asabar sun soma ne tun da sanhin safiyar kan unguwannin 'yan tawaye na wadannan birane inda suka hallaka fararan hula 25.