Jirgin Birtaniya ya tashi daga Masar a karon Farko
November 6, 2015Wani jirgin sama mallakar kasar Birtaniya dauke da fasinjoji 165 da ke zama 'yan yawon bude idanu na Birtaniya ya tashi a karon farko daga filin tashi da saukar jiragen sama na Sharm el-Sheikh na Masar a ranar Juma'an nan kamar yadda jami'ai a kasar ta Masar suka bayyana.
Shi dai wannan jirgi mai lamba EZY9854 ya tashi daga wannan filin jiragen sama inda ya nufi filin tashi da saukar jiragen sama na Gatwick da ke a Birtaniya bayan kuwa ya kwashe tsawon sa'oi ya na jira a ba shi dama.
A ranar Laraba ne dai kasar ta Birtaniya ta soke tasowar duk wani jirgi daga wannan kasa mai wuraren yawon bude saboda fargabar kada ko yana dauke da bam a cikinsa bayan kuwa jirgin saman mallakar kasar Rasha ya tarwatse a samaniya da a cewar Birtaniya an dana bam ne a cikinsa. Amma 'yan Birtaniya an basu damar komawa gida tare da daukar tsauraren matakai a ranar Jumma'an nan.