1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgi ya nutse da mutane 57 Mauritaniya

Abdul-raheem Hassan MNA
December 5, 2019

Hukumar kula da kaurar jama'a ta duniya IOM na aiki da hukumomin kasar Mauritaniya na ba wa wadanda suka tsira daga hatsarin jirgin ruwan kulawar gaggawa.

https://p.dw.com/p/3UFbi
Mauretanien Banc d Arguin National Park Fischerboote
Hoto: Imago Images/photothek/T. Imo

Mutane 150 ne ke cikin jirgin da ya fito daga kasar Gambiya. Bincike ya gano cewa mai ne ya kare wa jirgin ruwan yayin da ya doshi hanyar shiga Mauritaniya. Sai dai ba a bayyana inda jirgin ke da niyyar zuwa ba.

Yanzu haka dai hukumomin Mauritaniyan tare da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNHCR na aiki tare don samar da agajin gaggawa ga mutane 83 da suka tsira.