1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta fice daga cikin yarjejeniyar New Start

Abdourahamane Hassane
February 22, 2023

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce janyewar da Rasha ta yi daga cikin yarjejeniyar kawar da makaman nukiliya ta New Start wani babban kuskure ne.

https://p.dw.com/p/4NrG2
Polen Besuch Präsident Biden
Hoto: Czarek Sokolowski/AP/picture alliance

Shugaban na Amurka yana magana ne gabanin ganawa a birnin Warsaw na  Poland da shugabannin kasashe tara na NATO daga Tsakiya da Gabashin Turai. Rasha ta ce za ta iya sauya wannan dakatarwar ne, idan har Washington, wacce take zargi da aikata laifuka karya wasu dokokin da aka cimma ta nuna kyakyawan hali. An saka hannu a kan yarjejeniyar a shekara ta 2010, kuma ita ce  yarjejeniya ta karshe tsakanin Amirka da Rashar ta kwance damarar makaman nukiliya.