1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

John Dramani Mahama ne sabon shugaban Ghana

December 10, 2012

Jama'a a Ghana sun koma bakin aiki ba tare da samun wani tashin hankali ba biyo bayan bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasar.

https://p.dw.com/p/16z4e
Hoto: Getty Images

Bayyana sakamakon shugaba ƙasar Ghana ke da wuya sai magoya bayan jam'iyyar NDC ta shugaba John Dramani Mahama su ka ɓarke da sowa da waƙe-waƙe gami da kade-kade.

Da ya ke karanto sakamakon zaben, shugaban hukumar zaɓen ƙasar ta Ghana Dr. Kwadjo Afari Gyan ya ce John Dramani Mahama na jam'iyyar NDC mai mulki ya samu ƙuri'u miliyan biyar da dubu dari biyar da saba'in da hudu da dari bakwai da sittin da daya ko kuma kwatankwacin kashi hamsin da ɗigo bakwai cikin dari na kuri'un da aka kada yayin da Nana Akufo-Ado na jam'iyyar NPP ya samu ƙuri'u miliyan biyar da dubu dari biyu da arba'in da takwas da dari takwas da casa'in da takwas da wanda ke zaman kashi arba'in da bakwai na kuri'un da aka kaɗa.

Magoya bayan shugaba Mahama dai sun yi fatan shugaban ya kai ga cika alkawuran da ya dauka gami da tsayawa tsayin daka wajen ganin Ghana ta samu cigaba mai ma'ana.

Wiederwahl John Mahama in Ghana
Titunan birnin Accra sun cika da masu murna na NDCHoto: Reuters

A cikin zaɓuka shida da kasar ta Ghana ta gudanar tun bayan da ta koma bin tafarkin demokradiyya a shekara 1992, jam'iyyar NDC ta lashe zaben sau hudu kenan. Tuni dai kananan jam'iyyun siyasar kasar su ka yi mubayi'a ga shugaba Mahaman ko da ya ke dan takarar shugaban kasa na babbar jam'iyyar adawar wato Nana Akufo-Ado bai ce komai ba tukunna dangane da sakamakon.

Shi dai shugaba Mahaman zai gama wa'adin mulkinsa na wannan karo a ranar shidda ga watan Janairu kana a rantsar da shi a ranar bakwai ga watan Janairu domin jan ragamar mulki har zuwa shekara 2016.

Ghana Wahlkampf Nana Akufo-Addo
Madugun 'yan adawa Nana Akufo-AddoHoto: dapd

Mawallafiya : Rahmatu Mahmud Abubakar Jawando
Edita : Halima Balaraba Abbas

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani