1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jonathan: Sabbin dabarun ceto 'yan Chibok

May 30, 2014

Shugaban Najeriya ya dauki tsawon makonni biyu yana zaga kasashen waje da nufin samo hanyar warware matsalolin tsaro na cikin gida da kasarsa ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/1C9fd
Goodluck Jonathan
Hoto: AFP/Getty Images

Duk da cewar dai ya yi nasarar samun akalla sojoji dubu kan iyakar tarrayar Najeriya da Kamaru da ke gabas, tuni zirga-zirga dake shafar harkoki na gwamnati ta fara daukar hankali cikin kasar inda ra'ayi ke rabe ga wannan mataki na shugaban kasar.

Tschad Militär
Sojin kasashe makota za su tallafawa NajeriyaHoto: MIGUEL MEDINA/AFP/Getty Images

Engineer Buba Galadima jigo a cikin jam'iyyar APC da ke adawa, ya kuma ce ''maimakon a rinka dorawa wasu laifi a sani fa a jihohin Borno da Yobe da Adamawa an sa dokar ta baci, kuma karkashin wannan doka shi ne babban kwamandan askarawan kasar ke da ruwa da tsaki kan batun tsaro, idan ya kasa yin wani abu yanzu Ghana ce ko Equitorial Guinea ko Africa ta Kudu ce za ta shigo ta yi mana maganin wani abu''

To sai dai kuma a cewar Bello Sabo Abdulkadir da ke zaman sakataren kungiyar dattawan arewa maso gabashin, in yawo neman ceto bai amfana komai ba mai zai hana a nemi shawara da ka iya taimakwa ga kokarin tabbatar da karshen yakin da ke zaman ruwan dare gama duniya a halin yanzu.

''Ba za su iya samun wani sauki game da daukar yaran nan da aka yi a wannan yawo ba face daga baya a ce akwai maganar hadin gwiwa da nufin tare matsalar wadannan mutane masu ta'addanci, amma dan dai maganar kubutar da yara zai gama yawon duniya kaf sai ya dawo Abuja a Najeriya a nan za'a iya samun hanyar kubutar da yaran nan.''

Yayin da 'yan Najeriya ke cigaba da bayyana ra'ayoyinsu dangane da wannan sabon yunkuri na shugaban kasar wanda suke ganin ba zai kai ga amfanawa kasar da mai idanu ba, a hannu guda gwamnatin kasar na hangen samun nasara a burin da sanya a gaba.

Demonstration Boko Haram Nigeria 14.05.2014
Ana cigaba da gangami don ganin an sako daliban ChibokHoto: Reuters

Abun jira a gani dai na zaman tasiri na sabuwar dabarar ga Jonathan din da ke neman mafitar rikicin da sannu a hankali ke tashi daga matsalar talakawa zalla ya zuwa ga masu ruwa da tsaki da makomar kasar ta Najeriya baki daya.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita : Zainab Mohammed Abubakar