1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jordan da Masar sun yi kira ga farfaɗo da shawarwarin zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya.

September 10, 2006
https://p.dw.com/p/Bujv

Sarki Abdullah na ƙasar Jordan da shugaba Hosni Mubarak na Masar sun yi kira ga gamayyar ƙasa da ƙasa da ta ba da ƙaimi wajen farfaɗo da shawarwarin samad da zaman lafiya a yankin Gabas Ta Tsakiya. A wata ganawar da suka yi yau a birnin Amman, shugabannin biyu sun yarje kan cewar ba za a cim ma sulhunta rikicin larabawa da Isra’ila ba, sai an tinkari lamarin gaba ɗayansa bisa dogaro kan duk ƙudurorin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta zartar kan yankin da kuma kan shirin nan na bai wa larabawa ƙasarsu da Isra’ilan ta mamaye, don su ma a nasu ɓangaren, su amince da zaman lafiya. Kazalika kuma, sun ce yunkurin da ake yi a halin yanzu na farfaɗo da shawarwarin zaman lafiyar ya ci tura. Sabiili da haka ne dai ya kamata a samo wata sabuwar hanya ta tinkarar matsalar.

Tun da ƙungiyar Hamas ta lashe zaɓen Falasɗinawa a farkon watannin wannan shekarar ne dai ƙasashen Yamma suka dakatad da duk wasu shawarwari kan batun samad da zaman lafiya.