1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Julia Tymoschenko za ta tsaya takara

March 27, 2014

A shirye-shiryen zaben da ake yi a kasar Ukraine, tsohuwar firaministan kasar da ta shafe shekaru a gidan kaso ta bayyama aniyarta na tsayawa takara

https://p.dw.com/p/1BXUR
Ukraine Julia Tymoschenko Pressekonferenz
Hoto: AP

Tsohuwar firaministan Ukraine Julia Tymoschenko ta bayyana aniyarta na tsayawa takarar neman shugabancin kasar.

Mai shekaru 53 na haihuwar ta ce, ranar 29 ga watan Maris, za ta nemi damar tsayawa takarar daga jam'iyyarta ta Batkivshina.

Ana sa ran gudanar da zabukan kasar ne ranar 25 ga watan Mayu idan Allah ya kai mu.

Idan ba yanzu ba, 'yar siyasar mai goyon bayan manufofin Turai ba ta taba fitowa fili ta bayyana wannan aniya na ta ba.

A shekarar 2004 ta tsaya tare da shugaban kasa na baya-bayan nan Viktor Janukovich, inda suka kasance kan gaba a juyin juya halin da aka fi sani da Orange Revolution a turance.

A shekara ta 2010 kuma ta sha kaye daga abokin hammayanta mai goyon bayan manufofin Rasha, wato Viktor Yanukovich. Wanda daga hawan shi mulki ya sa aka kulle ta a gidan kaso na tsawon shekaru 7, sakamakon samunta da laifin amfani da mukaminta lokacin tana firaminista ta hanyoyin da basu dace ba.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar