1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jundullah ta dauki alkahin harin Karachi

Mouhamadou Awal BalarabeMay 13, 2015

Masu kaifin kishin Islama sun hallaka mutane da dama a Pakistan tare da shan alwashin ci-gaba da Kai hare-hare a Karachi da wasu birane na kasar

https://p.dw.com/p/1FPGu
Hoto: DW/R. Saeed

Kimanin mutane 43 sun rigamu gidan gaskiya a birnin Karachi na Pakistan a wani harin da 'yan bindiga suka kai a kan wani bas da ke dauke da tsirarun 'yan shi'an kasar. Tuni dai kungiyar Jundullah da ke da kaifin kishin Islama ta dauki alhakin wannan harin, da ke zama mafi muni a watanni hudu na baya-bayanan.

Wani babban jami'in 'yan sandan Pakistan ya ce 'yan bindiga shida da ke kan babura ne suka yi luguden wuta a kan direba da kuma mutane 60 da ke cikin motar da ya ke tukawa. Tuni dai hapsan hapsoshin sojojin kasar ta Pakistan Janar Raheel Sharif ya soke ziyarar aiki a Sri Lanka sakamakon wannan aika-aika.

Hare-haren na neman zama ruwan dare a birnin Karachi sakamakon haihawar ayyukan ta'addanci a Pakistan. A watan Disemban bara ma dai mutane 154 ne suka sheka lahira a Peshawar a lokacin da 'yan Taliban suka kutswa wata makaranta tare da bude wuta irin na kan mai uwa da wabi.