An yanke wa wasu sojoji hukuncin daurin shekaru 120 a Saliyo
August 11, 2024Rahotanni daga birnin Freetown na cewa alkalai bakwai da suka jagoranci zaman kotun sun tabbatar da hukuncin dauri na dogon zango ga sojojin bayan shafe kusan watanni takwas ana gudanar da shari'a kan zargin hannunsu a kifar da gwamnatin shugaba Julius Maada Bio a watan Nuwambar 2023.
Karin bayani: Saliyo: Koroma da ke daurin talala zai fita waje
A yayin arangamar sojojin sun bude wuta a babban birnin tare da kutsawa fadar shugaban kasa da barikin soji da kuma babban gidan yarin birnin Freetown inda fursunoni sama 2000 suka tsere.
Karin bayani: Saliyo: Ana tuhumar wasu mutane kan juyin mulki
Hukumomi a wancan lokacin sun tabbatar da cafke mutune sama da 80 da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulkin, ciki har da tsohon shugaban kasar Ernest Bai Koroma, wanda daga bisani kotu ta sallame shi bisa dalilan rashin lafiya.