Kabul: Bayan janyewar sojojin Amirka
A ranar 31 ga watan Augusta Amirka ta kawo karshen aikin sojojinta a Afghanistan bayan kusan shekaru 20. Babu tabbas yadda lamura za su kasance karkashin gwamnatin Taliban a kasar.
Mu fita
Suna daga cikin rundunar karshe ta sojojin kasashen waje da suka rage a filin jirgin saman Kabul. A ranar 31 ga watan Augusta, sojoji daga bataliya ta 82 ta sojin sama suka hau jirgin dakon kaya na sojin Amirka wanda ya kawo karshen aikin shekaru 20 mafi tsawo a tarihin Amirka na aikin sojojinta a kasar waje.
Taliban a filin jirgin sama
Washegari, 'yan jarida sun dauki hoton wata kungiyar mayakan Taliban a sashen tashin jiragen sama - ko kuma abin da ya saura daga gare shi. Filin jirgin saman Kabul shi ne kadai kafar sadar da Afghanistan da kasashen duniya. Dubban 'yan gudun hijira sun sami barin kasar a 'yan makonnin da suka wuce. Sai dai wasu 'yan Afghanistan din da dama an bar su a baya kuma yanzu ba su san makomarsu ba.
Dakatar da ci gaba da yaki
A garejin jirage a filin jirgin saman Kabul, jiragen yaki ne da suka lalace samfurin A-29 na sojin jiragen sama na Afghanistan. Rundunar sojin kasar na da dakaru 180,000 wadanda aka kashe biliyoyin kudade wajen ba su horo tare da mashawarta sojoji masu tarin yawa. Sai dai sakamakon janyewar sojojin kasashen waje, sojojin na Afghanistan sun daina aiki.
Taliban sun dare kujerar tukin jirgin sama
'Yan Taliban sun dare kan kujerar tukin jirgin yaki na Afghanistan. Bayan ficewar sojojin Amirka sun bar jiragen sama da dama da masu saukar ungulu wadanda ake tsammani ba za su sake aiki ba. Abin da ya saura ba kawai ya kasance tarkace ba ne kadai, yana ma sanya fargaba kan yadda makoma za ta kasance a karkashin mulkin masu tsattsaurar akida.
Shiri ya wargaje
Bayan lalacewar gaban jirgi mai saukar ungulu na sojin saman Afghanistan wanda ba za a iya gani ta cikinsa ba, babu tabbas a game da makomar kasar ita kanta. Da sauran aiki a gaban 'yan Taliban masu tsattsaurar akida kafin su iya kafa gwamnati. Babbar ayar tambaya ita ce yadda salon mulkin su na tsattauran ra'ayi zai kasance nan da 'yan makonni ko watanni masu zuwa.
Hattara, 'yan sintiri
Irin wadannan hotuna suna ko ina a Kabul. Mayakan Taliban dauke da makamai a kan tituna da gundumomi suna sintiri da motocin yaki masu sulke wadanda sojojin Amirka suka bari bayan da suka janye. Duk da dan sassaucin halayya da 'yan Taliban din suka nuna tun bayan da suka karbe ragamar iko 'yan makonni da suka wuce, 'yan Afghanistan da dama suna tsoron makomarsu da kuma ayyukan ramuwar gayya.
Makomar yara kanana
Wani dan tireda ke tafiya a titin birnin Kabul da balan-balan masu launuka. Makomar yara karkashin Taliban yana cikin rudani. A cewar kungiyar agaji ta duniya mai kula da rayuwar kananan yara mai suna World Vision, yara fiye da miliyan takwas a Afghanistan suna bukatar kariya da tallafin jinkai na gaggawa. Kungiyar ta ce suna cikin gagarumin hadari.
Gudunmawar mata
Bayan da sojojin kawance na kasashen yamma suka yi nasarar karfafa hakki da 'yancin mata a Afghanistan, a yanzu sun koma sanya Burqa kamar yadda ake ganin su a kan tituna. Babu tabbas ko wace nasarar ce za ta dore a sabuwar gwamnatin Taliban - wannan dai zahiri ne game da hakkin mata.
Aikin yau da kullum
Akalla a wasu yankuna, komai na daukar wani salo na dabam. Kamar wannan asibitin a Wazir Akbar Khan, mata da dama kwararrun jami'an asibiti suna kula da marasa lafiya. Mutane da dama ba su yarda da kalaman sassaucin ra'ayi na 'yan Taliban wadanda aka sani da tsattsaurar akida ba, wadanda a baya suka sha yin kalamai masu harshen damo game da 'yancin mata a tarukan manema labarai.
Damuwa kan talauci da tsadar rayuwa
Dogon layi a wajen wani banki. Mutane a yanzu suna fargabar faduwar darajar kudi. Afghanistan na daya daga cikin kasashe matalauta a duniya. Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Guterres ya yi kashedin aukuwar tagaiyarar al'umma a kasar. Kusan rabin al'ummar kasar sun dogara ga samun tallafi. Daya daga cikin mutane uku 'yan Afghanistan bai san inda zai sami abin da zai ci ba.