1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan haramta wa mata Jami'a

Zainab Mohammed Abubakar
December 22, 2022

Turkiyya da Saudi Arabiya sun kasance kasashen musulmi na baya-bayan nan da suka yi Allah wadan matakin gwamnatin Taliban na harantawa yara mata zuwa matakin karatu na jami'a.

https://p.dw.com/p/4LK6j
Afghanistan | Afghanische Studentinnen reagieren gegen das Studienverbot
Hoto: Bilal Guler/AA/picture alliance

Gomman mata ne dai a yanzu haka suke gudanar da zanga-zanga a kofar jami'ar Kabul, wanda ke zama gangamin adawa na farkon irinsa a bangaren al'ummar Afghanistan, tun bayan da Taliban din ta sanar da rufe kofar jami'ointa ga mata.

Tun jiya ne dai aka rika korar dalibai mata da suka je jami'a don daukar darasi, biyo bayan bayan umurnin da gwamnatin Afghanistan din ta bayar na cewar, daga yanzu an harantawa mata zuwa manyan makarantu a kasar.

Tuni dai kasashen ketare ke sukar manufofin gwamnatin Taliban din na kin bude makarantun sakandare na yara mata, tun daga watan Maris, matakin da ta yi alkawarin yin waiwaye a kansa.