1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin kaddamar da sabuwar gwamnatin Burkina Faso

Suleiman Babayo
February 11, 2022

An saka ranar da za a kaddamar da sabuwar gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso a mako mai zuwa wadda ta yi alkawarin magance matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/46u45
Burkina Faso | Paul-Henri Sandaogo Damiba
Hoto: Facebook/Präsidentschaft von Burkina Faso

An tabbatar da Lt. Kanar Paul Henri Sandaogo Damiba a matsayin sabon shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Burkina Faso, a cikin wata sanarwa da kotun kula da tsarin mulkin ta bayar a wannan makon.

Sannan a wannan Jumma'a wata sanarwar sojan kasar ta tabbatar da cewa an saka ranar Laraba mai zuwa 16 ga wannan wata na Febrairu a matsayin ranar da za a yi bikin kaddamar da sabon shugaban gwamnatin mulkin sojan, bayan juyin mulkin ranar 24 ga watan Janairu da ya kawo karshen gwamnatin Shugaba Roch Marc Christian Kabore.

Kanar Damiba ya yi alkawarin samar da tsaro a kasar ta Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka wadda take fuskantar hare-hare daga kungiyoyin masu nasaba da kishin addinin Islama. Sakamakon juyin mulkin an dakatar da kasar ta Burkina Faso a kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma da kungiyar Tarayyar Afirka.