Kaddamar da wasannin Olympics a Pyeongchang
February 9, 2018'Yan wasan motsa jiki fiye da 2900 da suka fito daga kasashe daban-daban na duniya za su fafata domin neman manyan kyaututa 102 da aka tanada ga wasanni 15. Gasar ta bana ta da Koriya ta Kudu ta kira ta da sunan gasar zaman lafiya, ta bada damar kusantar juna tsakanin Koriyar da Kudu da makwaciyarta kuma babbar abokiyar gabatarta Koriya ta Arewa. A farkon ranar ne kuma aka yi babbar ganawa mai tarihi tsakanin shugaban kasar ta Koriya ta Kudu Moon Jae-in, da Shugaban jeka na yi ka na Koriya ta Arewa Kim Yong Nam, sannan da kaunar shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Yo Jong da ke wakiliyar shugaban na Koriya ta Arewa mai cikeken iko Kim Jong Un.
Sai dai kuma bikin ya rage armashi bayan da mataimakin Shugaban Amirka Mike Pence wanda ya jagoranci tawagar Amirkawa zuwa Koriya ta Kudun, bai halarci zaman cin abincin da Koriya ta Kudun ta shirya kafin soma gasar ba. Ga tsarin da aka yi dai mataimakin shugaban na Amirka zai zauna ne a teburi daya kuma kusa da kusa da shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in, da kuma shugaban jeka na yi ka na Koriya ta Arewa Kim Yong Nam.