Kafar sada zumunta "Threads" ta fara aiki
July 6, 2023Talla
Kamfanin Meta ya jinkirta kaddamar da kafar Threads a nahiyar Turai saboda rashin samun izini daga hukumomin Brussels na Kungiyar Tarayyar Turai. Sabuwar kafar sada zumuntar wani bangare ne na Instagram da ke zama wani reshe na kanfanin Meta, kuma yana iya amfanar da mutane sama da biliyan biyu, kuma ba a tanadi amfani da tallace-tallace a wannan kafar ba ya zuwa yanzu.
sai dai sa'o'i hudu bayan kaddamar da Threads, Shugaban kanfanin Meta Mark Zuckerberg ya bayyana cewar fiye da mutane miliyan biyar sun yi rejista. Dama kanfanin Meta na fatan zama sabon dandamalin aikewa da sakon da aka fi so a duniya, lamarin da ka iya dakushe Twitter.