1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama tsakanin China da Taiwan

Abdourahamane Hassane
September 18, 2023

Hukumomin Tsibirin Taiwan sun ce fiye da jirage sama guda100 ne da na ruwa na yaki guda tara aka gano a kusa da yankin cikin sa'o'i 24 suna shawagi a gewayen tsibirin.

https://p.dw.com/p/4WSL5
Hoto: Jason Lee/REUTERS

Wata sanarwar offishin minstan cikin gida na Taiwan ta ce, ci gaba da yin barazanar na sojojin China zai iya haifar da tashin hankali da tabarbarewar tsaro a yankin. Ma'aikatar cikin gidan ta Taiwan ta yi gargadin, tana mai kira ga hukumomin China da su dakatar da wadannan munanan ayyuka da suka kira tsokana. Tun a shekara ta 1949 kasashen biyu ke yin rikiciwandaChina ta yi ikirarin cewar yankin mallakarta ne.

China-Taiwan Militärübung
Hoto: picture alliance/Xinhua News Agency