1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunusiya: Sabon kundin tsarin mulki

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 26, 2022

Rahotanni na nuni da cewa al'ummar Tunusiya sun amince da sabon kundin tsarin mulki a kasar da zai karawa Shugaba Kais Saied karfin iko.

https://p.dw.com/p/4EeGG
Tunusiya | Shugaban KAsa | Kais Saied
Shugaban Tunusiya Kais Saied ya yi murnar yadda zaben rabar-gardama ya kayaHoto: AFP

Cikin wani rahoto da kamfannin bincike da tattara bayanai na Sigma Conaeil ya fitar, ya nunar da cewa kaso 92 cikin 100 na kuri'un da aka kada sun nuna amincewa da sabon kundin tsarin mulkin. Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta kasar ta bayyana cewa, bayan da 'yan adawa suka kauracewa zaben kaso 27 da digo biyar na al'ummar kasar da suka cancanci kada kuri'a ne kacal suka fito domin kada kuri'unsu a zaben. Zaben raba-gardamar kan sabon kundin tsarin mulkin dai, zai bai wa Shugaba Saied damar korar jami'an gwamnati daga aiki da nada alkalai da kuma bai wa sojoji umarni. Tsohon kundin tsarin mulkin da aka amince da shi a shekara ta 2014 a Tunusiya dai, ya bai wa firaminista karfin iko fiye da shugaban kasa.