Fayulu ya ce zai je kotu kan zaben Kwango
January 11, 2019Wannan kiran na zuwa daidai lokacin da mutumin daya zo na biyu a zaben Martin Fayulu ya ce zai kalubalancin sakamakon zaben a gaban kotu. Martin Fayulu hamshakin dan kasuwa da ya yi suna wajen sukar matsalar cin hanci da rashawa da ta zama ruwan dare a Kwango, ya fada wa daruruwan magoya bayansa da suka hallara a Kinshasa babban birnin kasar ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango cewa ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar na ranar 30 ga watan Disambar 2018, da hukumar zaben kasar CENI ta ce Felix Tshisekedi ne ya lashe. Fayulu ya ce a ranar Asabar za su yi gangami a gaban babbar kotun kasar.
Kasar Faransa da kasar Beljiyam wadda ta yi wa Kwango mulkin mallaka, sun saka ayar tambaya game da sakamakon zaben, yayin da kasar Amirka ta yi kira da a yi cikakken bayani bayan da majami'ar Katholika da ta tura jami'an sa idon zabe su kimanin dubu 40, ta ce sakamakon da hukumar zaben Kwango wato CENI ta sanar bai yi daidai da wadanda jami'anta suka tattara ba. Didier Reynders shi ne ministan harkokin wajen kasar Beljiyam da ya ce kasarsa na sa ido kan abin da ka iya faruwa a Kwango, kuma kasar na aiki kan wani shiri na kare baki matukar rigima ta barke a Kwango.
Ita dai hukumar zaben a Kwango wato CENI ta ayyana daya daga cikin 'yan takarar 'yan adawa Felix Tshisekedi a matsayin wanda ya lashe zaben, sai dai Emerie Damien Kawira shugaban kawancen wani gungun 'yan siyasar Kwango mai mazauni a birnin Brussels na kasar Beljiyam ya ce akwai wani shiri a boye tsakanin Shugaba Joseph Kabila da Tshisekedi.
Idan aka tabbatar da sakamakon, to zabe zai zama irinsa na farko da za a mika mulki ta hanyar dimukuradiyya a Kwango.