Kallo ya koma kan Amirka a taron G20 na birnin Bonn
February 16, 2017Manufofin harkokin waje na sabuwar gwamnatin Amirka na zama abin da aka zura ido a ga inda suka nufa. Dama dai manyan jami'ai na kasashen da suka fi karfin arziki sun ta jira su ga kamun ludayin sakataren harkokin wajen kasar ta Amirka Rex Tillerson.
Tillerson ya kasance farin wata sha kallo a zauren taron na birnin Bonn, wannan shi ne karon farko da ya halarci taron G20. Dama kuma takwarorinsu na kasashe masu ci gaban masana'antu sun kasa fahimtar alkiblar da sabuwar gwamnatin Amirka ta dosa kan lamuran da suka shafi manufofin harkokin waje. Saboda haka ne Tillerson ya yi keke da keke da ministocin kasashen da suka nuna shakku kan dangataka tsakaninsu da Amirka musamman ma China da Jamus.
Amma kuma batu da ya fi daukar hankali shi ne dangantakar Amirka da Rasha kasancewa shugaban Donald Trump na daukar takwaran aikinsa na Rasha Vladimir Putin da kima. Hasalima dai ministocin harkokin wajen kasashen biyu Rex Tillerson da Serguei Lavrov sun yi alkawarin yin aiki da nufin kyautata mu'amalar da ke tsakaninsu.
Ministan harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson ya yaba kamun ludayin Amirka dangane da manufofinta na ketare, inda ya ce wannan ya nuna cewar ba za a farfado da yakin cacar baka tsakanin kasashen biyu karkashin Shugabancin Trump ba. Tuni ma dai fadar mulki ta Kremlin ta zaku ta ga cewar hulda tsakaninta da Washington ta inganta, musamman ma bayan zaman doya da manja da aka samu karkashin shugabancin Barack Obama.
Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya yi kira da a farfado da aikin hadin gwiwa tsakanin hukumomin leken asiri na kasashensu domin yakar ayyukan ta'addanci gadan-gaban. Sai dai kuma ya yi gargadin cewar duk wani mataki na nuna karfi daga gwamnatin Amirka zai iya rusa wannan tsari.
Idan za a iya tunawa dai China da Amirka sun kasance a sahun gaba na kasashen da gwamnatin Amirka ke suka game da manufofinsu na kasuwanci, inda ta ce salon kasuwancinsu ne ke dankwafar da tattalin arzikin Amirka.