Zaben Amurka: Kalubalen Kamala Harris
August 20, 2024Birnin Dearborn da ke jihar Michigan a Amurka, na dauke da mutane masu tsatso da kasashen Larabawa. Birnin ya kasance guda daga cikin yankunan da ke da muhimmanci wajen samun kuri'un da zai iya bai wa dan takara damar yin zarra, musamman a zaben Amurka da ke da zafi. A wannan birni akwai wani shagon sarrafa kayan makulashe da abubuwan tande-tande, wadanda galibi aka san Larabawa na ta'ammali da su. Shagon mai suna Masri Sweets mallakin wani dan kasuwa ne wato Khadar Masri da ya kwashe shekaru sama da 30 yana aiki, kuma ma'aikatansa na da tushe da Gabas ta Tsakiya da arewacin Afirka. Yakin da ke faruwa a Zirin Gaza, abu ne da ke daukar hankali matuka cikin hirarrakin da ake yi a kullum a wannan waje a cewar Khadar Masri. Yayin da Balaraben dan kasuwa Masri ke cewa zai zabi Kamala Harris a zaben na Amurka, su kuwa masu sayen kayayyakin shagonsa na da ra'ayoyi mabambanta ne a kan 'yar takarar ta jam'iyyar Democrats.
Duk da cewa dai Larabawan mazauna Amurka Musulmi ne da kuma Kirista suna da wata cibiya da ke hada mutane da dama a ranakun Jumma'a, inda suke gudanar da ayyuka na ibada. Sufian Nabhan, shi ne shugaban cibiyar yada addinin Islama a birnin Detroit da ke cikin jihar ta Michigan, kuma ya ce mazauna wannan yankin na cikin matukar bakin ciki saboda kashe-kashen 'yan uwansu maza da mata a yankin Falasdinu. Baya ga shi wannan limamin, akwai ma wasu da ke bayyana wannan ra'ayi irin nasa. Tuni dai Donald Trump ya riga ya bayyana abin da zai yi kowa ya san kudurinsa, su kuma 'yan jam'iyyar Democrats na ta rawar 'yanmata. Shigowar 'yar takarar jam'iyyar Democrats Kamala Harris ya sauya tafiyar siyasar Amurka musamman a yanzu, sai dai kuma a fili yake cewa a jihar ta Michiga tana da sauran aiki a gabanta.