Kalubalen da ke gaban Sharif na Pakistan
May 13, 2013Da sanyin safiyar Litinin din nan ce (13.05.2013) hukumar zaben Pakistan ta fidda sakamako na wucin gadi na zabukan da aka yi a kasar a ranar Asabar din da ta gabata inda sakamakon ke cewar jam'iyyar Pakistan Muslim League ta Nawaz Sharif ta samu kujeru tamanin da tara daga cikin kujeru dari da hamsin da takwas da aka kidaya na daukacin kujerun majalisar dokokin kasar dari biyu da sittin da tara.
Jam'iyyar PTI ta tsohon dan wasan kurket din nan Imran Kahn wadda ake zaton za ta taka rawar gani a zaben kuwa a halin yanzu ta tsira ne da kujeru ashirin da daya yayin da ja'iyyar PPP ta marigayiya Benezir Bhuto ke biye mata da kujeru sha takwas.
Fitar wannan sakamako na wucin gadi dai wanda ya sanya jam'iyyar PML ta Nawaz Sharf kan gaba ya sanya shi da magoya bayansa fara shagulgula na yin nasara duk kuwa da cewar jam'iyyar PTI ta Imran Khan na zargin an tafka magudi, yayin da a hannu guda al'ummar kasar su ka fara hangen irin kalubalen da ke gaban sabuwar gwamnatin da za a kafa.
Zahid Hamid da ke zaman kuma guda cikin wanda su ka sanya idanu kan zaben na Pakistan kana mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a kasar ya ce a hangensa kalubalen tsaro ne zai kasance babbar matsalar da sabuwar gwamnatin kasar za ta fuskanta.
Ya ce ''Pakistan na fama da matsaloli iri daban-daban amma abun da zai zamto babban kalubale ga sabuwar gwamnatin kasar shi ne batun samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar musamman ma dai a wuraren da ake fama da tashe-tashen hankula da kuma wuraren da masu kaifin kishi addini ke cin karen su ba babbaka''.
Baya ga batun tsaro, dangantaka da Pakistan da sauran kasahen duniya wani abu ne da zai zamto kalubale ga sabbin mahukuntan kasar kasancewar Nawaz Sharif na da banbanci ra'ayi da mahukuntan kasar da su ka gabata musamman ma dai irn dangantakar kasar da yammacin duniya duba da cewar jam'iyyar Mr. Sharif na da ra'ayi ne irin na mazan jiya kamar yadda Imtiaz Ahmad, mai sharhi kan al'ammuran yau da kullum a kasar ya shaida.
Ya ce ''dangantarmu da kasashen ketare za ta zama wani babban kalubale musamman ma dai batun yaki da ta'addanci da ire-iren hari da a kan kai da jiragen nan marasa matuki kana sabuwar gwamanti za ta fuskanci kalubale irin na karancin wutar lantarki.''
Sha'ani na tattalin arziki ma na daga cikin kalubalen da gwamnatin kasar za ta fuskanta musamman ma dai a yanzu haka da tattalin arzikin kasar ke kwan-gaba kwan-baya, to sai dai a wani yunkuri da ya yi na ba zata Nawaz Sharif ya nada Ishaq Dar wani tsohon ministan kudin kasar a matsayin wanda zai sake darewa kan wannan mukamin, batun da ya sanya hannayen jarin birnin Karachi na kasar wanda ke zaman cibiyar kasuwancin Pakistan su ka kara daraja a wannan Litinin din.
Wannan ya sanya Zahid Hamid ganin cewar matsalar ta tattalin arziki ka iya kasancewa mai saukin warwarewa ga gawamnatin.
Ya ce ''kamar yadda aka sani dan kasuwa ne saboda haka ina ganin zai yi gyare-gyare masu yawa da nufin fitar da kasar daga kangiya da tsinci kanta na tabarbarewar tattalin arziki''
Yanzu haka dai abin jira a gani shi ne irin fitar cikakken sakamakon zaben na Pakistan da irin gwamnatin da Nawaz Sharif zai kafa gami da irin kamun ludayin da sabuwar gwamnatin da kuma irin dangantakar da za a samu tsakin gwamnatin da 'yan adawa musamman ma dai jam'iyyar PTI ta Imran Khan da kuma jam'iyyar PPP ta Benazir Bhuto wadanda ke da karfin fada a ji a fagen siyasar kasar.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Saleh Umar Saleh