1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Kenya: Kalubalen fitar da gahwa Turai

September 25, 2024

Kamfanin African Coffee Roasters da ke sarrafa kofi ko gahwa a kasar Kenya, na zaman guda daga cikin manyan kamfanoni da suke sarrafa shi su fitar da shi zuwa kasashen Turai. Sai dai sabuwar dokar EU na son kawo cikas.

https://p.dw.com/p/4l4MJ
Kenya | Kofi | Kericho
MAnoman kofi ko gahwa cikin fargaba a KenyaHoto: Billy Mutai/ZUMAPRESS/picture alliance

Sabuwar dokar kungiyar Tarayyar Turan EU kan kwararowar hamada da za ta fara aiki a karshen wannan shekara, na haifar da fargaba ga kamfanonin da ke sarrafa kofi din ko gahwa a kasashen gabashin Afirka. Dokar dai ta tanadi cewa duk kamfanin da ke son ya tura ganyen kofi din ko gahwa zuwa nahiyar Turai, tilas ya kasance wajen da aka shuga shi bai fuskanci matsalar zaizayar kasa a shekaru hudu da suka gabata ba. Guda daga cikin ma'aikatan kamfanin sarrafa kofi din na Kenya African Coffee Roasters Jane Kamau ya nunar da cewa, wannan sabuwar doka babban kalubale ce ga kananan manoma da ke samar da 'ya'yan kofi din ko gahwa a baki dayan yankin na Gabashin Afirka. David Muhia manomi ne a kauyen Kiambu da ke da nisan sa'a guda da Nairobi babban birnin kasar ta Kenya wanda ke noman gahwa din da dankali da fiya da ayaba da sauran kayan amfanin gona, kuma a cewarsa a yanzu tilas kamfaninsu na hadaka ya sanya kudi kimanin Euro 3,500 domin yin rijistar yankin da suke noma ga wani kamfani mai zaman kansa. Wannan kamfanin dai, shi ne wanda zai bayar da shaidar da kungiyar ta EU ke bukata kan wuraren da aka noma amfanin gonar. Ba dai Muhia ne kadai ke fuskantar wannan matsalar ba, manoma da dama a yankin gabashin Afirkan na fama da ita.