1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rundunar G5 Sahel na fuskantar tarnaki

Ramatu Garba Baba GAT
July 3, 2018

Shekaru kusan biyu bayan kafa rundunar G5 Sahel da nufin yakar 'yan ta'adda a yankin Sahel, har yanzu tana fuskantar tarnaki wajen gudanar da ayyukanta.

https://p.dw.com/p/30l9t
Sahel Konflikt - Malische Armee
Hoto: Getty Images/AFP/D. Benoit

Tun a watan Nowamban shekarar 2015, shugabanin kasashen biyar na yankin Sahel suka sanar da samar da rundunar soji guda da suka yi wa lakabi da G5 Sahel. An kafa rundunar ne, don yakar ayyukan ta'addanci da wasu da ke gudanar da ayyukan da ke wa zaman lafiya karan tsaye. Sai dai jim kadan bayan soma aikinta rundunar ta fara fuskantar manyan kalubale da suka soma saka shakku a zukatan jam'a da ke ganin da wuya a iya cimma muradun kafa wannan runduna a sabili da munanan hare-haren da ake samu duk da kasancewarta a yankin. 


A makon da ya gabata, an kai wani mummunan harin ta'addancin a hedikwatar rundunar tsaron G5 Sahel da ke a kasar Mali, harin da ake ganin tamkar watsa kasa ne a idanun kasashe biyar na Mali da Burkina Faso da Nijar da Chadi da kuma Mauritaniya da suka samar da rundunar da ta kunshi sojoji akalla dubu biyar. Lamarin ya ja hankalin duniya dama wasu da ke yin kira na ganin an sauya dabarun tunkarar wannan barazanar tsaron.

Babban magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres na daga cikin wadanda suka yi wannan kira inda ya ke cewa:

'' Rundunar G5 Sahel na bukatar karfafawa da wasu sabbin dabaru, da kuma uwa uba tallafi na kudi ba kakkautawa. Da hakan za ta iya aikinta na yakar ayyukan ta'addanci da wadannan kungiyoyi na masu tayar da kayar baya''

Mauretanien Frankreich Afrikanische Union
Hoto: picture-alliance/L.Marin

Daman an dauki matakin samar da rundunar ce, don ta cike gibi a gudanar da wasu ayyuka da rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali wato Minusma ba ta da hurumin yi, misali minusma ba ta da karfin ikon yakar 'yan ta'adda. Shin kwalliya ta biya kudin sabulu a wannan fannin? Abdelhak Bassou dan asalin kasar Moroko ne kuma masanin siyasar yankin na Sahel, a nashi fadin rundunar ce ta ragwaye:

"Abin da na ke nufi shi ne a sake karfafa rundunar tun daga tushe. Ba yadda za a iya kafa runduna mai karfi ba tare da an horas da sojojinta ba tun daga tushe ba. Shekaru biyar ana horas da na Mali, za a iya cewa an sami ci gaba kenan, to haka ya ke ga sauran kasashen Nijar ko da Burkina Faso'' 

Ana ganin akwai gazawa kwarai da gaske, la'akari da karfin sojojin da ke kunshe a rundunar.  Akwai batun hadin kansu da irin horon da suka samu tun daga kasashensu, wannan zai sa a fahinci kalaman sakataren Majalisar Dinkin Duniya Gueterress na samar da sabbin dabaru da kuma neman karin tallafi 

Mali Besuch UN Generalsekretär Antonio Guterres
Hoto: Getty Images/AFP/S. Rieussec

Batun wadata rundunar da kudi ya kasance abin da ake son ganin an yi kuma cikin gaggawa kafin wanki hula ya kai dare. Batun da ko a taron koli na Kungiyar Tarrayar Afirka da ya gudana a birnin Nouakchott na Moritaniya, an jaddada bukatar samar wa rundunar kudi maimakon kiraye-kiraye da aka saba na bayar da goyon baya da yin Allah wadai da hare-haren ta'addancin. Ewan Lawson masani ne da ke nazari kan sha'anin tsaro na rundunar hadin gwiwa, ya ce yana cike da fata za a iya kai wa ga samun nasara, sai dai hakan na bukatar lokaci:

" Idan an kwatanta da kungiyar tsaro ta NATO sama da shekaru sittin ko saba'in ta dauka tana aiki na karfafa rundunar a tsakanin kasa da kasa. A yankin Afirka ma hakan mai yiyuwa ne kuma mun kamo hanya don abu ne mai yiyuwa".

An dai kammala taron AU na bana da fatan ganin an samu ci gaban raba yankin da ayyukan kungiyoyi da suka buwayi yankin da munanan hare-hare.