Kalubalen yarjejeniyar sauyin yanayi
November 7, 2016A ranar 4 ga watan Nowamba, 2016 aka fara aiki da yarjejeniyar kare sauyin yanayi da akacimma a birnin Paris. Wannan yarjejeniya dai ta samu amincewar manyan kasashe da su ka hada da Amirka da China da suke taka muhimmiyar rawa wajen fitar da gurbataccen hayaki da ke lalata muhalli. Wannan taro karo na 22 wato COP 22 na birnin Marrakesh da ke Moroko da aka fara a wannan Litinin zai gudana har tsawon mako guda inda ake fatan kammala shi a ranar 18 ga wannan wata na Nuwamba.
Laurent Fabius shi ne ya jagoranci taron birnin Paris da ya amince da yarjejeniyar da kasashen suka cimma:
"Ina neman taron ya amince da wannan matsayi mai taken yarjejeniyar Paris. Ina kallon martani na amincewa. ban ji wanda ya nuna turjiya ba, an amince da yarjejeniyar birnin Paris."
Da haka daukacin kasashen da suka halarci taron suka amince da yarjejeniyar kan rage fitar da hayaki mai gurbata yanayi a sararin samaniya. Kuma daga bisani kasashen sun bi matakin da ya dace domin amincewa da yarjejeniyar wadda za ta taimaka wajen dakile iska mai dumama duniya nan da shekara ta 2030, abin da zai rage dumamar duniya da ake samu. Daukacin kasashen da su ka rattaba amincewa da yarjejeniyar ne su ka sake haduwa a birnin Marrakesh na Moroko domin jaddada kudirin.
Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya nuna karfin gwiwa kan cimma burin da ake bukata wajen taron musamman bayan nasarar da aka samu kan fara aikin da yarjejeniyar birnin Paris na Faransa:
"Babban kalubalen shi ne karfin gwiwa da za mu ci gaba da shi zuwa aiwatar da yarjejeniyar. Ba mu da lokaci, amma yarjejeniyar Paris kan ci-gaba mai dorewa, ya sa duniya ta na da wani shiri kan rage fitar da gurbatacciyar iska kan sauyin yanayi."
Mr Ban ya kara da cewa a shekarun da suka gabata an yi hadaka kan sauyin yanayi. Jami'an gwamnati, da masana kimiyya, da shugabannin addinai, da shugabannin 'yan kasuwa da kungiyoyi masu zaman kansu cikin kasashen duniya sun fahimci cewa makomar jama'a a duniya na cikin tsaka mai wuya. Shugaban Kiristoti mabiya darikar Katolika na duniya Papa-Roma Francis ya na cikin shugabannin addininai da su ka nuna farin ciki da fara aiki da yarjejeniyar ta birnin Paris da kuma kakkyawar fata kan taron na birnin Marrakesh na Moroko da aka fara a wannan Litinin:
"Kwanakin da suka gabata aka fara aiki da yarjejeniyar birnin Paris kan sauyin yanayi. Wannan ya nuna mutane za su iya aiki tare domin kariya da kirkiro tattalin arziki kan zaman lafiya da adalci."
Karkashin yarjejeniyar ta Parisduk kasar da za ta fice daga aiwatar da yarjejeniyar sai ta shafe shekaru hudu kafin ta yi hakan a hukumance.