1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban taron hadin kan kasa a Kamaru

Dirke Köpp ATB/MNA
September 30, 2019

Masu ruwa da tsaki da suka hada da gwamnoni da sarakunan gargajiya da shugabannin addinai sun yi ta tururruwa zuwa zauren taron da ke Yaounde.

https://p.dw.com/p/3QVyk
Kamerun Wahl l Präsident Paul Biya
Hoto: picture alliance/dpa/j. Warnand

A kasar Kamaru a wannan Litinin aka fara babban taron hadin kan kasa domin sasanta rikicin da ya dabaibaye yankunan Ambazoniya da ke magana da harshen Turancin Ingilishi. Rikicin da ya balle a shekarar 2016 ya haddasa hasarar rayukan mutane kusan 3,000 yayin da wasu kimanin dubu 500 suka yi kaura daga gidajensu.

Masu ruwa da tsaki da suka hada da gwamnoni da sarakunan gargajiya da shugabannin addinai suka yi ta tururruwa zuwa babban birnin kasar. Babban burin shi ne gudanar da babban taron kasa da aka fara a wannan Litinin.

Daruruwan 'yan Kamaru daga ko ina a fadin kasar har ma da 'yan kasar da ke zaune a kasashen waje gwamnati ta gayyace su domin taimakawa wajen gano bakin zaren warware rikicin yankin na Kamaru da ke magana da harshen Ingilishi.

A ranar 12 ga watan Oktoban 2016 ne dai rikicin ya barke a yankunan kudu maso yamma da arewa maso yamma bayan da lauyoyi da malaman makaranta suka fito zanga-zangar adawa da gwamnati, wadda suke gani ta mayar da yankin na Ingilishi saniyar ware yayin da gwamnatin ta mayar da martani da tsauraran matakai domin shawo kan zanga-zangar.

Paul Atanga wani na hannun daman shugaban kasar Paul Biya ya fito karara yana Allah wadai da masu zanga-zangar yana mai cewa babu wata matsala a yankin da ake magana da harshen Ingilishi illa dai cewa masu zanga-zangar 'yan tada zaune tsaye ne wadanda wasu mutane daga waje da ke juya akalarsu suka saye su da kudi.

Kardinal Christian Tumi ya yi korafi game da rashin kyakkyawan shugabanci
Kardinal Christian Tumi ya yi korafi game da rashin kyakkyawan shugabanciHoto: DW/F. Muvunyi

Wani malamin addinin Kirista a yankin Anglophone da ake magana da harshen Ingilishi Kardinal Christian Tumi da ke zama masu karfin fada a ji a kasar ya shaida wa DW musabbabin wannan rikici.

"Tushen wannan rikici ya samo asali ne daga rashin shugabanci na gari. Ba a shigar da jama'a a shawarwarin da ake dauka alhali sune a tsakiyar harkar gudanarwar siyasa da sha'anin mulki da wanda muka aro daga Faransa."

Sai dai rage karfin iko na gwamnatin tarayya domin bai wa yankunan kwarya-kwaryar dama na daga cikin dalilan tashin hankalin a ra'ayin wani malamin addinin kirista na darikar Presbyterian Thomas Mokoko Mbue

"Matsalar yankin Anglophone da ke magana da harshen Ingilishi matsala ce wadda ta dade tun kafuwar kasar Kamaru. Tun shekarar 1961 ake ta yiwa gwamnati kiraye-kiraye, korafi iri-iri domin zama a tattauna amma ta ki sauraron kowa har sai da abu ya kazance."

Sanin ko yara nawa ne a cikin kungiyar 'yan awaren ta Abazoniya yana da wuya, sai dai wasu na kiyasin cewa adadin ya kama daga 200 zuwa 2000 sun kuma karkasu zuwa kananan rassa kama daga reshen 'yan kasar waje da ke zaune a Amirka da Norway da sauransu kamar yadda Thomas Makoko ya nunar.

"Wasu yaran ba su ma kai shekaru 15 da haihuwa ba. Abin takaici ne cewa wadannan yara kanana da ya kamata su zama manyan gobe suna mutuwa a yakin da bashi da amfani."

Nkongho Felix Agbor Balla na son a duba batun tsarin tarayya na Federaliyya
Nkongho Felix Agbor Balla na son a duba batun tsarin tarayya na FederaliyyaHoto: CHRDA

Sai bayan da aka shafe shekaru uku da bukatun farko da 'yan yankin Ingilishin suka gabatar kana bayan da rikicin da ya kassara dubban jama'a sannan ne shugaba Paul Biya ya yi kiran gudanar taron kasa domin tattauna hanyoyin samun masalaha.

Wani lauya mai rajin kare hakkin bil Adama Félix Agbor Balla kuma daya daga cikin wadanda suka shirya zanga-anga ta farko a 2016 ya ce taron kasar da za a shafe kwanaki biyar ana gudanarwa a Yaounde zai duba batun tsarin tarayya na Federaliyya.

"Tun fil azal rikicin ya fara ne da neman ba da kwarya kwaryar cin gashin kai. Idan ba ta attauna yanayin gwamnatin da ake so a kasa ba to kuwa ba za mu sami mafita ba."

Babu tabbas ko 'yan Ambazoniya za su tura wakilai zuwa taron. Gwamnati dai ta aika wa shugabannisu goron gayyata, to amma da dama sun sa kafa sun yi fatali da taron wanda suka ce shirme ne kawai da bata lokaci da kuma barnatar da kudin harajin talakawa kamar yadda shugaban yan awaren Mark Bareta ya wallafa a shafinsa na Facebook. Yana mai cewa gwamnati ta san abin da yankin Anglophone da ke magana da Ingilishi suke bukata saboda haka ba sai sun kara bata wani lokaci ba.