1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Gangamin rigakafin zazzabin cizon sauro

Zakari Sadou
January 22, 2024

Kamaru ta kaddamar da gangamin rigakafin zazzabin cizon sauro, matakin da ya mayar da ita kasa ta farko da ta jagoranci wannan aiki a yunkurin yaki da cutar

https://p.dw.com/p/4bYxO
Stechmücke auf Hautoberfläche
Hoto: picture-alliance/dpa/Center for Disease Control/J. Gathany

Jirirai 'yan watanni 6 da dama ne aka yi wa rigakafin farko na zazzabin cizon sauro kyauta a babban asibitin Douala a gaban wakilin gwamnan yankin Littoral. Babban asibitin Douala na daya daga cikin cibiyoyin kiwon lafiya da aka zaba inda iyaye za su kai yaransu domin karbar allurar. Daya daga cikin iyayen yaran da aka yi wa rigakafin da ta bukaci a sakaya sunanta ta bayyana farin cikinta da rigakafin.

Gangamin na Kamaru na zuwa ne bayan gwajin allurar rigkafin cutar a kasashen Ghana da Kenya, wanda masana suka tabbatar da tasirin rigakfin wajen kare yara daga kamuwa da cutar.

Rigakafin Malaria a Datcheka Kamaru
Rigakafin Malaria a Datcheka KamaruHoto: Desire Danga Essigue/REUTERS

Aurelia Nguyen shugabar shirye-shirye a kungiyar the Gavi Vaccines Alliance wadda kungiya ce da ke taimaka wa Kamaru wajen samun rigakafin ta ce akwai yara rabin miliyan ko wacce shekara da ke mutuwa sanadiyar zazzbin cizon sauro, yanzu mun shiga lokaci da za a raba rigakafin a kasashen Afirka, mun fara maida hankali ne inda aka fi bukata, Kamaru ta kasance kasa da ke fama da cutar.

A cewar hadakar Gavi yanzu haka kasashe 19 ne za su fara amfana da rigakafin a wannan shekarar kadai. Kasar wadda ke tsakiyar Afirka na sa ran yi wa yara 250,000 rigakafin a bana da shekara mai zuwa.

Feshin maganin sauro
Feshin maganin sauroHoto: Mortuza Rashed/DW

Bayan tababar kusan shekaru 40 wajen tantance sahihancin rigakafin cutar ta Maleria, hukumar lafiya ta Duniya WHO ta amince da allurar rigakafin zazzabin cizon sauro da za ta zama cikakkiyar kariya ga illar da cutar ke yi a Kamaru musamman a nahiyar Afirka. Simplice Kengne wakilin gwamnan yankin Littoral a taron fara gangamin kaddamar da allurar rigakafin a Douala ya bukaci hadin kan kungiyoyin fararen hula a wannan gangamin

"Ina jan hankalin kungiyoyin fararen hula da jami'an kiwon lafiya da sarakunan gargaji da su bayar da hadin kai domin wannan gangamin yayi nasara"

Ya kuma bukaci tabbatar wa al'umma ingancin wannan allurar rigakafin domin kawar da wasu jite-jite da ke yaduwa wanda yake barazana ga lafiyar yara

Shirin yaki da zazzabin cizon sauro
Shirin yaki da zazzabin cizon sauroHoto: World Mosquito Program

Muna gayyatar iyayen yara da bai wa ‘ya'yansu damar a yi musu allurar a wuraren da aka kebe na musamman domin yaransu su amfana da wannan kyauta 

Wani rahoto da hukumar lafiya a Kamaru ta fitar a 2022 ya nuna cewa yara sama da miliyan shida sun kamu da cutar yayin da yara sama da dubu hudu zuwa 11 zazzbin cizon sauro ke kashewa ko wacce shekara, akasarin su yan kasa da shekaru biyar. 

A watan Nuwamba 2023 Kamaru ta karbi kashin farko na rigakafin zazzabin cizon sauro, Mosquirix wanda kamafani sarrafa magunguna na kasar Birtaniya GSK ya samar.