'Yan awaran sun ce ba za su halarci taron sulhun ba
September 12, 2019Talla
Bisa al'ada dai sau uku a shekara Shugaban Kasar Kamaru Paul Biya yake jawabi ga 'yan kasar. Amma rikicin da aka kwashe tsawon shekaru uku ana yi da 'yan aware a yankunan masu amfani da harshen Ingilishi ya sa shugaban ya sanar da cewar za a gudanar da babban taron tattaunawa domin samun bakin zaren warware rikicin a karshen wannan wata na Satumba. Sai dai an samu martani mabambamta kan jawabin na Shugaba Biya. Simon Ntonga mai nazarin harkokin siyasa ne a Kasar ta Kamaru da ya yi fatan cewa shugaban zai cika alkawarin da ya dauka. Ya ce: "A karon farko ina iya cewa mun gano cewa da gaske shugaban kasar yake a kan abin da ya fada da kuma yake tunani, zai tabbatar da dukkan alkawuran da ya yi a cikin sanarwar."